Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSaduwa ko taba mace ba tare da yardar ta ba fyade ne...

Saduwa ko taba mace ba tare da yardar ta ba fyade ne a dokar Najeriya ko da mijinta ne

Daga Muryoyi

Daga yanzu za a iya hukunta mazajen da matansu suka kaisu kara bisa zargin sun yi masu fyade, hakan na zuwa ne sakamakon gyara da akayiwa dokar fyade wato VAPP Law, yanzu mace na iya tuhumar mijinta da yi mata fyade kuma a hukunta shi.

Dokar da aka gyra ana ce mata VAPP LAW wato ma’ana “Violence Against Persons Prohibition law

Da yake karin haske game da yadda dokar take a yanzu, wani babban lauya kuma tsohon kakakin kungiyar lauyoyi ta kasa NBA reshen Benin, Douglas Ogbankwa ya ce daga yanzu ba sai mutum ya samu damar saduwa ne za a tuhumeshi da fyade ba “ko tattaba mace bisa rashin da’a yanzu fyade ne”

- Advertisement -

Kafin gyaran dokar VAPP dai a Najeriya baya yiwuwa mace ta kai karar mijinta da sunan yayi mata fyade amma yanzu an gyara dokar

Muryoyi ta ruwaito a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, Douglas yace an kara fito da ma’anar fyade wanda hakan zai rage yawan shaidun da a baya kotu ke nema idan aka gurfanar da mai laifi da ya shafi fyade “a yanzu ko sautin murya aka dauka indai a ciki anji kururuwar dake alamta cewa namiji na shafar mace ko yana yi mata tabe-tabe a jikinta na rashin da’a za a kama mutum da laifin fyade”

A cewarsa “ba sai an saka azzakari cikin farji ne fyade ba kamar yadda aka saba daga yanzu ko taba jikin mace fyade ne”

Lauyan ya cigaba da cewa kuma a yanzu an amince miji ko mata na iya tuhumar juna idan dayansu ya kusanci daya ba tare da amincewarsa ba ko daya ya taba wa daya jiki na sha’awa da bai amince ba. Hakan shima fyade ne kuma za a yi hukunci akai muddin aka shigar da kara.

Mista Ogbankwa ya ce “Dokar VAPP a yanzu ta yi tanadin “fyaden ma’aurata” ko miji ko mata daya na iya tuhumar daya da laifin yayi masa fyade kuma ayi hukunci akai.

Fyade ba sai an sadu ba ko tabe-tabe ma fyade ne, Lauyan ya ce gyaran dokar ya saukake wa hukumomi wajen neman shaida idan an kama mutum da zargin fyade “ko sautin murya aka samu dake nuna wani jinsi ya taba wani jinsi tabawar rashin da’a ya wadatar ayi hukuncin fyade” inji mista Ogbankwa

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: