Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSai da mukayiwa ‘yan Nigeria kashedin sake zaben Buhari a 2019 amma...

Sai da mukayiwa ‘yan Nigeria kashedin sake zaben Buhari a 2019 amma ba’a ji mu ba –Dr Hakeem

Daga Muryoyi

Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ce dama sai da suka ja kunnen yan Arewa kan sake zaben Buhari shugaban kasa a karo na Biyu a 2019 amma sukayi kunnen shegu “Munyiwa ‘yan Nigeria kashedi da karawa Buhari wasu shekaru hudu a 2019, amma ba’a ji mu ba.”

Dr Hakeem yana bayani ne a cikin wani takaitaccen sako da ya fitar domin wayar da kan matasan yanzu da yace wasu na hure masu kunne suna yiwa dattawan Arewa gurguwar fahimta a duk lokacinda suka bayyana ra’ayinsu ko sukayi wata sanarwa

“Mun ci gaba da kare mutumcin Arewa, tun lokacin da Buharin ya kan zauna da mu, har yazo idan mun yi magana sai dai abi mu da munanan maganganu, ko a saka sa’oin jikokinmu su rika zagin mu. A yanzu haka Kungiyar mu sai hamdala, kuma muna rokon Allah Ya bamu magada su ci gaba daga inda zamu tsaya.”

- Advertisement -

“Ko shekara daya da hawan Buhari mulki ba ayi ba na lura dama shi mukamin shugaban kasan yake so, ba yiwa kasa da talaka hankoro ba”

“Akwai wadanda sukan rasa abin da zasu ce mani idan na nuna gazawar Shugaba Buhari sai kawai suce ina adawa ne domin bai saka ni cikin gwamnatin sa ba. Wannan ba abin mamaki ba ne, domin abinda ake gaya masu suce ke nan kawai.

Wadanda ke basu abin fadi basu da abu daya da zasu fada masu su fadi na karya ko sharri akan abubuwan da nakan fada akan gwamnatin Buhari.

Ni saboda Buhari na shiga siyasa bayan na gama aikin gwamnati a jiha da tarayya, kuma naga yadda gwamnatin Jonathan take daukar mulki ba yadda ya kamata ba, musanman ma matsalolin da suka shafi Arewa. Buri na kawai shine in bada gudummuwa a cire Jonathan a samu Buhari ya zama shugaban kasa ya gyara Arewa da Nigeria. Ban taba aiki da Buhari ba, amma kamar miliyoyin mutane, muna da zaton zai iya gyara Nigeria da Arewa da taimakawa talakawa.

Na shiga CPC saboda ita ce jam’iyyar Buhari a shekarar 2012. Na zama Chairman na CPC a Jihar Kaduna, da kuma muka hade da AC muka zama APC, aka sake zabe na shugaban APC Jihar Kaduna. Ofis dina a Kaduna shine headquarter na jam’iyyar har shekara Uku, har sai da na sauka da kaina a shekarar 2014.

A shekarar 2014, General Buhari ya roke ni in taimaka masa in saka ido a dukkan harkokin zabe da abubuwan da suka shafi INEC, kuma na yarda. Na koma Abuja na tsunduma wajen fafitikar neman nasarar APC, kuma Allah Ya amshi addu’ar mu Ya bawa shugaban kasa Buhari nasara, kuma muka sami gwamnoni da ‘yan majalisa da yawa, muka kori Jonathan da PDP.

Ni a waje na sai hamdala, burina na shiga siyasa ya cika. Ban taba saka raina a mukami ko wani aiki a gwamnatin Buhari ba, bamu kuma taba maganar bani wani aiki da shi ba. Ni a gani na wanda duk yayi ritaya lafiya, kuma yana da abinda zai tafiyar da iyalin sa, babu wani aikin da zai nema.

Aiki daya kawai na roki Allah Ya bani, shine in koma University in ci gaba da koyarwa kamar yadda nake yi kafin in koma aikin gwamnati. Buhari na zama shugaban kasa naje KASU a matsayin Asso Prof mai ziyara.

Ba’a yi ko shekara daya ba da hawan shugaban kasa Buhari mulki, sai na lura cewa shi mukamin shugaban kasan dama yake so, ba ya yi wa kasa da talaka hankoro ba. Shekaru da nayi na aikin gwamnati shekara 25, (wanda suka hada da rike mukamin Permanent Secretary har shekara 10) sun bani dama in fayyace ingantaccen shugaba da kuma shugaban da bai damu da jama’a ba.

A lokacin ne na yanke shawarar fita daga jam’iyyar APC, bayan na shaida wa wadanda muke APC AKIDA (watau masu neman a dawo hanya) cewa a ganina Buhari da gwamnoninsa basu da niyyar aikin da ya kamata suyi.

Babu gaba ko hamayya tsakanina da Shugaba Buhari da na kusa da shi. Matsalar itace ta ko dai in saka ido in yi shiru, ko kuma na cigaba da abin da yasa na shiga siyasa, watan taimakawa wajen tsare mutuncin Arewa da Jama’ar Nigeria, har iyakan karfi na. Na samu shiga Kungiyar Dattawan Arewa, kuma na godewa Allah dattawan kirki masu kishin Arewa sun yarda dani har sun bani mukamin kakakin su.

Na godewa Allah da ya zabar mani abubuwan da suka fi man amfani, wanda suka hada da kauce wa gwamnatin da yau ake ta kuka da ita a Arewa. Ni dan PRP ne, kuma ban taba zama dan PDP ba. Nayi aikin Chief of Staff na Sen Saraki, kuma na godewa Allah a kan irin samun fahimtar aikin majalisa wanda duk aikin da nayi ada ban samu ba.

Alhamdulillah, Allah Ya albarkaci aikin da muke yi a Kungiyar Dattawan Arewa. Munyi yakin siyasa na goyon bayan Buhari, kuma yayi nasara. Munyi wa ‘yan Nigeria kashedi da karawa Buhari wasu shekaru hudu a 2019, amma ba’a ji mu ba. Mun ci gaba da kare mutumcin Arewa, tun lokacin da Buharin ya kan zauna da mu, har yazo idan mun yi magana sai dai abimu da munanan maganganu, ko a saka sa’oin jikokinmu su rika zagin mu. A yanzu haka Kungiyar mu sai hamdala, kuma muna rokon Allah Ya bamu magada su ci gaba daga inda zamu tsaya.

Na fadi wannan takaitaccen tarihi ne domin ina ganin ana yaudarar matasa ana masu karerayi a kan mutane irin mu wadanda kan tsaya suce an yi daidai ko ba’a yi ba. Ni a yanzu bana bukatar komi sai ganin karshen irin halin da Arewa ke cikin, da samun mutanen da zasu canji wadannan shugabannin wadanda basu damu da talaka ba.

Ina rokon wadanda kan ji zafin an zage ni, kada su rama. Ni na yafe wa duk mai zagina ko wani batanci. Nima ina rokon gafarar wadanda nayi wa laifi.

Allah Ya iya mana abin da ba zamu iya ba, Yasa mu bambamta gaskiya daga karya.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: