Sarkin Daura ya auri yar shekara 20 zai kara daya Amaryar a karshen wata

Daga Muryoyi

Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk mai shekara 90 a duniya, ya auri sahibarsa yar kimanin shekara 20 da haihuwa mai suna Aisha Iro Maikano, an daura auren a ranar Asabar.

Rahotanni da Muryoyi ta tattaro ya nuna yarinyar diyar Fagacin Katsina ce Iro Maikano kuma an daura Auren ne a bisa sadaki Naira Miliyan Daya.

Magajin Garin Daura, Musa Umar, ne ya amso wa Sarkin auren.

- Advertisement -

A gefe daya kuma ana yada rade-radin cewa Amare biyu ne Sarkin zai aura ana sa rai nan da mako mai zuwa ko karshen wata za a daura daya auren wato amarya ta Biyun. Majiya ta shaidawa Muryoyi cewa “kwarai da gaske muna sa rai ranar Asabar mai zuwa ko kuma nan da karshen wata za a daura auren daya amaryar”

Muryoyi tayi kokarin jin ta bakin masarautar Daura kan wannan Aure da daya auren da ake rade-radin za ayi amma bamu samu dama ba, kawo yanzu dai ana jiran martanin masarautar na gasgatawa ko karyata lamarin

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: