Daga Muryoyi
Hukumar kula da Sahihancin Magunguna da Abinci a Najeriya, NAFDAC ta ce shan maganin ƙarfin maza na iya jawo mutuwar fuju’a watau mutuwar gaggawa.
Kazalika shan magungunan karfin mazan kan jawo cutar ɓarin jiki wato “paralys”
A sanarwar da hukumar ta fitar dauke da sanya hannun Darakta Janar Adeyeye NAFDAC ta nuna rashin jin daɗin ta game da yadda magungunan karfin maza su ka cika kasuwannin magani a faɗin ƙasar nan.
- Advertisement -
A cewar ta, yawancin irin magungunan ma ba su da rijistar NAFDAC ɗin. “Shigo da su a ke yi ta ɓarauniyar hanya,”
A Najeriya maza suna riƙa shan magungunan kara karfin saduwa domin su burge matan da su ke saduwa da su inda a wasu lokutan ake macewa ana tsaka da saduwar