Shatu Garko daga jihar Kano ta lashe gasar Sarauniyar kyau ta Nigeria
Daga Muryoyi
Wata budurwa yar shekara 18 daga jihar Kano Shatu Garko ta lashe gasar wacce ta fi kowace mace kyau a Nigeria a gasar bana da akayi a jahar Lagos
Muryoyi ta ruwaito Shatu ta doke abokan karawar ta su 18 inda ta zama Sarauniyar kyau ta Nigeria zango na 44 da akayi ranar Juma’a a Lagos
Kenan a halin yanzu Shatu ita ce budurwar da tafi kowace mace kyau a Nigeria wato Sarauniyar kyawawa
- Advertisement -