Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSheikh Bala Lau yace Gwamnatin na bakin kokarinta kan tsaro komawa ga...

Sheikh Bala Lau yace Gwamnatin na bakin kokarinta kan tsaro komawa ga Allah shine kawai mafita

Daga Muryoyi

Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi karin haske game da umurnin da ya bayar ga limaman Juma’a da na Kamsu Salawat da sauran dukkan masallatan Ahlussunah da ke fadin Nigeria na su fara gabatar da addu’o’i da Al-Qanutu a dukkan masallatai.

Muryoyi ta ruwaito Bala Lau na cewa
“Yawaita Istighfari da kaskantar da kai da addu’oi yana sa a warware maku da matsala na tsaro da karyewar tattalin arziki, in kun roki Allah kukayi isthfari Allah zai gafarta maku zai karbi addu’oin ku”

A cewarsa “Muna ta gaya wa alumma cewa komawa zuwa ga Allah shine kawai mafita ga halin da muka samu kanmu a ciki, a cigaba da addu’oi ba nan ba hatta mata a gida su ma su dauki Qur’ani su karanta kuma ayi ta zikiri ana azkarai ana ambaton Allah”

- Advertisement -

“Ai tayi ana kasakantar da kai ana rokon Allah har sai Allah ya yaye mana wannan bala’i”

Bala Lau wanda ya ce Gwamnatin na bakin kokarin ta akan matsalar tsaro ya kara da cewa “Gwamnati na iya kokarin ta, tana yin iya abunda take iyawa sai dai bata iyayi ita kadai sai kuma al’umma sun shigo ciki idan Gwamnati sunayi, kullum zaka ji sun ce anyi kaza an dauki mataki kaza, to menene mu kuma zamu taimaka domin wannan matakai da suke dauka ya zamanto an samu sauki”

“Shi abokin gaba sai ka ganshi kake iya daukar mataki akansa amma addu’a ko ka ga abokin gaba ko baka ganshi ba addu’a tana maka aiki. Idan su suna daukan mataki na makamai na don kokarin dakile abunda suke iya gani to mu kuma mu taya su da addu’o’i har ma abunda basu gani ba Allah yayi mana maganinsa”

Muryoyi ta ruwaito Kungiyar Izala ta bayar da umarnin a fara A-ƙunutu a dukkan masallatan Ahlussunnah da ke fadin Najeriya a kan matsalar tsaro

Sanarwar ta ambato Sheikh Bala Lau yana cewa: “Haka zalika dukkan majalis na ilimi da karantarwa da halƙoƙi na ilimi da haddar Al Qurani Mai girma da duka nau’uka na addua, duka muna ba da ummurni a ci gaba da yin addu’o’i.

“Haka ma mata a gida su ma su bi wannan umarnin da yawaita azkar da fatan Allah ya tausaya wa wannan al’umma.

“Idan mun yi wannan da kyakkyawar niyya muna zaton Allah zai amsa mana ya yi maganin ƴan ta’adda da masu daukar nauyinsu, kuma za a samu zaman lafiya a yankunan da matsalar tsaro ta shafa insha Allah,” in ji shi.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: