Sheikh Bello Yabo ya gargadi Buhari zai jagoranci zanga-zanga muddin aka kara kudin mai

Daga Muryoyi

Sheikh Bello Yabo Sokoto yace zai jagoranci zanga-zangar adawa da shirin Gwamnatin Najeriya na sayar da Litar mai a kan Naira 345 a shekarar 2022.

Muryoyi ta ruwaito a wani bidiyi an ga Malamin a lokacin da yake mayar da martani kan shirin gwamnatin tarayya na kara kudin mai a 2022, Malam Yabo yace “Lallai idan aka kai litar mai 345 da mu za a fitowa ayi zanga-zanga domin rainin wayon da rashin imanin yayi yawa, Indai a zamanin baya Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iya jagorantar zanga-zanga don an sayar da litar mai N65 kafin ya hau mulki, to lallai wannan lokacin da yake shirin kai ta N340 har [bore] ya kamata a yi ba zanga-zanga kawai ba domin rainin hankalin yayi yawa.” Inji Shi

Malam Bello Yabo Sokoto yayi waɗannan kalaman nasa ne lokacin da yake gabatar da wa’azin a masallacin Markazus Sunnah dake Sakkwato.

- Advertisement -

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: