Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSheikh Kabiru Gombe ya fadi abunda yasa Malamai basa sukar Gwamnatin Buhari...

Sheikh Kabiru Gombe ya fadi abunda yasa Malamai basa sukar Gwamnatin Buhari a mumbari

Daga Muryoyi

Babban Malamin Addinin Musulunci a Nigeria, Sheikh Kabiru Gombe ya yi karin haske kan dalilin da yasa malumma ba sa sukar Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari akan mumbari kamar yadda sukayi wa tsohuwar Gwamnatin Goodluck Jonathan.

Muryoyi ta ruwaito Shehun Malamin ya ce haramun ne garesu su caccaki Gwamnatin Buhari a mumbari saboda shi ya bude masu kofa suyi masa nasiha kuma yana sauraren su idan sun bashi shawara sabanin Jonathan wanda daga shi sai mutanen shi

Sheikh Kabiru Gombe a wani faifan bodiyo ya ce “Wani dan siyasa ya kirani yace Allah gafarta Malam muna mamaki shi wannan dattijon (Buhari) kuna bashi uzuri amma shugaban kasar da ya wuce mai malafa (Jonathan) bakwa bashi uzuri, sai ku fito kuyi magana akanshi a mumbari, me yasa?

- Advertisement -

“Nace kayi tambaya mai ma’ana, nace idan shugaba ya bude kofarsa ya ce ku zo ku fada mini gaskiya, inda nayi daidai ku fada mini inda nayi ba daidai ba ku fada mini, Haramun ne ku zage shi akan mumbari, Haramun ne kurakuransa ku ce akan mumbari zaku fada, ina zaku fadi kura-kuran?”

“Sai ku je ku kai mashi, nace wannan dattijon ya bude kofa duk lokaci sai ya sa an taro malumma su zo su fada masa ina kuskurensa ina daidai dinsa ya ke, kuma idan aka zo kowane malami sai ya bashi dama yayi magana. Na lissafo masa wasu abubuwa…. Wanda akayi taro da malumma suka nusar dashi (Buhari) kuma ya aiwatar.”

Muryoyi ta ruwaito Shiekh Gombe na cigaba da cewa har albarka shugaba Buhari ke saka masu idan sun fada mashi gaskiya “Yace Allah ya saka maku da alkhairi ku ke kusa da talakawa na gamus kuma zan dauki mataki. Na lissafa masa wasu abubuwa nace to damar da Gwamnatin yar malafa bata bayar ba kenan har ya gama Gwamnati ya sauka idan kaga yana taro da Malumma to Malumman addininsa ne, bai bude kofa ba.”

‘Idan shugaba ya kulle kofa babu dama a shigo a fada mashi to nan babu wani zabi “sai mu hau mumbari muyi masa fadam dama alaihim rabbuhum bizambihim fasawwaha….”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: