Shugaba Buhari ya taya Zago murnar zama shugaban APC Jihar Kano

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban APC bangaren su Sanata Ibrahim Shekarau, Ahmadu Zago murnar zama shugaban APC Jihar Kano,

Bayanin hakan ya fito ne a hirar Zago da majiyar Muryoyiya jim kadan bayan da shugaban APC ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar.

Zago yace “Shi [Shugaban kasa] ya tambaye ni ‘me aka samu?’, ni kuma na ce masa ‘an samu shugabancin APC a Kano. Daga nan ne ya taya ni murna'”,

- Advertisement -

Sai dai Muryoyi ta tattaro daga majiyar ta cewa basu tattauna kan rikicin da jam’iyyar take fama da shi a jihar Kano ba, a yayin ganawa da shugaban kasar “tun da batun yana kotu ba mu tattauna a kansa ba. Ka san shugaban kasa ba ya shiga lamarin da ke gaban kotu.” Inji Ahmadu Zago

Muryoyi ta ruwaito kodayake kawo yanzu ana kotu tsakanin bangaren Gwamnan Kano Ganduje da yan aware na bangaren Shekarau amma duk da haka shugaban ce musanta jita-jitar da ke cewa akwai yiwuwar su hade da tsohon gwamnan jihar ta Kano, Rabi’u Kwankwaso,

A cewar Ahmadu Zago “babu wannan batu. Sai dai ka san ita siyasa babu masoyi ko makiyi na dindindin.”

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: