Daga Muryoyi
Tsohuwar mai tsaron gidan kungiyar kwallo ta Nigerian (goalkeeper), Rachael Aladi Ayegba, ta koma sana’ar kabo-kabo da Bas a Ingila,
Muryoyi ta ruwaito Ayegba ta yi suna a lokacinda kakar wasan kofin duniya na mata a shekarun 2007 da 2006 da Kofin zakarun kasashen Afrika a 2008. Bugu da kari tayi wasa shekaru 11 a babbar kungiyar wasa ta kasar Finland, ta lashe babbar kyauta a 2013
Rahotanni sun ce a yanzu tsohuwar yar wasan ta koma tuka bas daga Lewisham zuwa Victoria na kasar Ingila
- Advertisement -
Yar Shekara 35, Ayegba ta shaidawa jaridar Standard UK ta kasar Amurka cewa ta daina kwallo saboda girma ya zo mata ‘kuma dama zamani kowa da nasa’ a cewar ta sana’ar tukin mota a yanzu ya fi mata kwanciyar hankali da rufin asiri.