Daga Muryoyi
Allah ya yiwa Sheikh Mas’ud Hotoro, ɗaya daga cikin Malaman da suka yi muƙabala da Sheikh Abdul-jabbar Nasiru Kabara rasuwa a sanadiyyar hadarin mota.
Daraktan harkokin addini na jihar Kaduna Malam Jamilu Albanin Samaru Zaria da wasu Malamai a Kano sun tabbatar da faruwar lamarin,
Muryoyi ta ruwaito Shehun Malamin ya gamu da ajalinsa ne a sakamkon hadarin mota a hanyar Kaduna zuwa Kano da sanyin safiyar yau Alhamis.
- Advertisement -
Shehin malamin dai babban masanin Kur’ani ne, kuma ya shahara musamman ga mabiyar darikar Kadiriyyah kuma yakan gabatar da karattukan addini da-dama a Kano, sannan shine ya wakilci kadiriyya a wajen mukabalar.
Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro daga ɓangaren ɗariƙar Ƙadiriyya kuma tsohon ɗalibin Sheikh Abduljabbar an fafata dashi sosai a wajen mukabalar