Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWani barawon babur a Kano ya sake shiga hannun hukuma Sati 6...

Wani barawon babur a Kano ya sake shiga hannun hukuma Sati 6 da fitowarsa Kurkuku

Daga Muryoyi

Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke wani mutum Usman Uzairu, Dan Shekara 57 bisa yunkurin satar Babur a wani Banki a layin Faransa dake karamar hukumar Fagge ta jahar Kano.

Wakilin Muryoyi ya ruwaito cewa Uzairu Dan asalin Garin Dayi ne dake jahar Katsina, Kuma mako 6 kenan da fitowarsa daga gidan kurkuku bayan ya shafe shekara Biyu a tsare bisa laifin sata da sayen kayan sata.

Kakakin rundunar yansanda ta jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa bidiyon mutumin a shafinsa na Facebook inda a ciki yake cewa ansha kama mutumin akan aikata satar babur a lokuta da dama da kuma sayen kayan sata.

- Advertisement -

Barawon Babur din yace sharrin shaidan, A cewarsa a da can shi direban motane sai ya rasa motar tun a lokacin da yayi hatsari ya rasa motar dalilin da yasa ya koma yin sata kenan, ya kara da cewa ya sha yin sata a jihohin Kano da jahar Bauchi da Gombe da kuma cikin garin Katsina, ya ce kimanin shekara 10 kena yana sata kuma kawo yanzu ya saci babura sun kai Goma.

Tsohon ya kara da cewa shekaru da dama matansa suka barshi saboda yana yin sata “Matan nawa sun tafi sun ce ba zasu iya zama da barawo ba, amma wannan shine na karshe ba zan sake sata ba” inji shi

Muryoyi ta ruwaito mutumin na yawa da makullan masta key da yake amfani dasu wajen bude baburan da yake son ya sata.

Sai dai Muryoyi ta ruwaito Kiyawa na cewa Kwamishinan yan sanda reshen jihar Kano, Sama’ila Dikko, ya bahar da umurni a yi kwakkwaran bincike sannan a gabatar da wanda ake zargin a gaban kotu.

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: