Daga Muryoyi
Wani mutum a kasar Koriya ta Kudu ya daskarar da gawar mahaifiyarsa inda yake fatan a nan gaba kimiyya zai dawo mata da ranta.
Mutumin wanda aka sauya sunansa na asali zuwa Jung-kil yace bai taba zaton mahaifiyarsa zata mutu ba.
Muryoyi ta kalli wani faifan bidiyo da wata jarida ta wallafa inda ta jiyo Kim na cewa “Don haka yaki yiwa gawar jana’iza kuma zai ajiye ta har zuwa shekara 100 masu zuwa”
- Advertisement -
Margayiyar ta kamu da cutar kansa kuma ta mutu a shekarar 2020 tana da shekara 80
Gawar mahaifiyar Jung-kil na cibiyar daskarar da gawa ta Moscow, Kim yace ta mutu kasa da watanni 6 da rasuwar mahaifinsa
“Mahaifiyata jaruma ce ban taba zaton mama zata mutu ba” cewar Kim cikin shessheka
Muryoyi ta ruwaito rahoton da BBC ya fitar ya nuna a duniya baki daya akwai gawarwarki 600 da aka daskarar dasu, mahaifiyar Kim itace ta farko a Koriya ta Kudu