Daga Muryoyi
Wani babban attajiri shugaban rukunin kamfanin gidaje na Shona Group a Florida dake kasar Amurka, Masoud Shojaee ya gwangwaje matarsa da dankareren jirgin sama wato “Private Jet” a matsayin kyautarsa ta bikin Kirsimeti
Muryoyi ta ruwaito matar attajirin ce mai suna, Stephanie Shojaee ta sanya bidiyon lokacinda mijin nata ke yi mata kyautar a shafinta na Instagram tana cike da zumudi
A bidiyon da ta sanya an ga lokacinda mijin mata ya sauke ta a wata babbar mota baka a tashar jiragen sama kusa da wani jirgi kana ya kwance kyallen da ya daure mata fuska dashi domin ta ga kyautar bazata da yayi mata.
- Advertisement -
Stephanie ta rubuta “Wayyo Allah na!! Mijina yayi Mista Masoud Shojaee yayi mani mahaukaciyar kyauta ta kololuwa, Ina son ka. Yau shekara 11 da aurenmu amma sai da kayi mani kyautar bazata!”