Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWasu Gwamnoni basu ji dadi da na Gina makarantum tsangaya ba --inji...

Wasu Gwamnoni basu ji dadi da na Gina makarantum tsangaya ba –inji Jonathan

  • Daga Muryoyi

    Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan yace wasu gwamnoni basuji dadi ba lokacin da ya gina makarantun tsangaya a wasu jihohin Arewacin Nigeria.

An yi rade-radin Gwamnatin Jonathan ta gina makarantun tsangaya akalla guda 35 acikin wa’adin mulkinsa na farkon na shekara biyu.

Wakilin Muryoyi ya ruwaito a lokacin dayake gabatar da lacca a wajen bikin yaye daliban da suka halarci kwas din gudanarwa na hukumar leken asiri a cibiyar harkokin tsaro ta kasa dake Abuja, a ranar Alhamis, Jonathan ya bayyana almajirai a matsayin kadangaren bakin tulu.

Mista Jonathan a don haka ya roki Gwamnonin jahohi 19 na Arewa dasu gyara tsarin karatun almajirai awani yunkuri na magance matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta.

Jonathan ya kara da cewa yayi rokon ne domin ganin cewa ba nauyin Gwamnatin tarayya bane gina makarantun firamare da kula da su don haka Gwamnonin suyi bakin kokarinsu don ganin sun kula da sha’anin tsangaya da almajiranci a jihohinsu.

“A halin da ake ciki ko almajirai sun kammala karatu a tsangaya za kaga ko a karamar hukumarsu ba za a dauke su aiki ba saboda haka a basu dama suyi karatun addini da na zamani wato Boko. A inganta sha’anin tsangaya a zamanatar dashi” inji Jonathan

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: