Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYan bindiga sun kai hari kauyen wani Dan-a-mutun Buhari sun sace danginsa...

Yan bindiga sun kai hari kauyen wani Dan-a-mutun Buhari sun sace danginsa bayan yace “mulkin Buhari kwalliya ta biya kudin sabulu!”

Daga Muryoyi

Yan bindiga sun sace dangin wani dan gani kashenin Buhari wanda ya rika yin mugun fata kan duk masu adawa da Gwamnatin Buhari da kuma neman yin zanga-zanga kan tabarbarewar rashin tsaro a Nigeria

Muryoyi ta ruwaito a cikin abubuwan da wannan matashi mai suna Surajo Saidu Sokoto ya rika fadi har da cewa “La’akari’ ‘da ‘yanda Shugaban kasarmu Buhari ya fatattakar cin “Hanci ‘Da Rashawa Nigeria a cikin shekaru 6 kacal.
Mu kam zamu ‘iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu!. Alhamdulillah”

Sannan a lokacinda aka shirye zanga-zangar nuna bacin rai da kisan mutane a Arewa Surajo ya rika babatu da yin mugayen addu’a kan masu fita zanga-zangar har ma yana cewa “Yan Nigeria minene amfani kiyayya da Buhari don Allah?

- Advertisement -

Allah yasa jami’an tsaro su wargaza duk wata zanga-zanga da yan Nigeria suka shirya yiwa Buhari”

Kwatsam kuma sai gashi yau da safe a gigice yana rikon a taya su da addu’a domin a daren jiya yan bindiga sun kai hari kauyensu har ma sunyi awon gaba da yan uwansa fiye da su Biyar.

Surajo a kidime ya rubuta cewa “Cikin juyayi ‘da bakin ciki ‘nake sanar da ‘Yan uwana musulmi.

A garinmu na Kwasare dake Wurno Local Gwamment Sokoto cikin ‘dare jiya wasu marasa tsoron Allah
Sunyi awon gaba ‘da ‘yan uwan Haihuwata “fiye ‘da Biyar
INA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UON!”

Sai dai Muryoyi ta ruwaito nan da nan sai ga mutane sama da Dubu sunyi masa martani wato comment amma fa marasa dadi, domin kadan daga cikin comment da muka dauko:-

“INSHA ALLAHU SAURA KAI ZAKA SHIGA MASIFAR DA BAKA TABA TUNANINTA BA .

KUMA SU DA AKA KWASHE SU INDA BABARKA A CIKINSU SAI ANYI MATA FYADE KACHA KACHA SAN NAN SU JEFAR DA ITA ALLAH YA WADARANKA – inji wani Usman S Adam

“Kaje ka Jagoranci DSS kubi hanyar da suka bi ku nemo su amma naso ace Kai aka sace” –inji wani Ibrahim Umar

“Uban giji Allah yazama gatansu kai kuma Allah yasa su daukeka Dan darajar Annabi Muhammad saw” inji wani -Dan Asabe Westman

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: