Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYan bindiga sun sace dangin Mai yawan cewa mulkin buhari kwalliya ta...

Yan bindiga sun sace dangin Mai yawan cewa mulkin buhari kwalliya ta biya kudin sabulu kuma zai jagorancin DSS gidajen masu zanga-zanga ko adawa kan tsaro

Daga Muryoyi

Da alama wankin Buhariyya ya biyo kan wani dan A Mutum Buhari Surajo Saidu Sokoto da yayi kaurin suna wajen adawa da duk mai sukar Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bayan da yan bindiga suka kai hari kauyensu suka kwashe danginsa fiye da Biyar.

Cikin abubuwan da Surajo ya rubuta a kwanan nan sun hada da:-

“Muna ‘Goyon Bayan Jami’an Tsaron Nigeria. ‘Da Su Kama ‘Duk Wani Mugun Malamin Da ‘Ya ‘Yiwa Shugaba Buhari

- Advertisement -

Alkunuti A Masallacinsa Gobe Ranar Jummu’a!”

Sannan ya rubuta “Ni Dakai Na Zan Jagoranci Hukumar DSS Ta Fara Kama Masu Zagin Buhari A Facebook Cikin Jaharmu Ta Sokoto Gida-Gida Billahillazi Mafiyawa Duk Nasansu”

Saidu ya cigaba da cewa “Duk Musulmin Da Kaji Yace Laifin Buhari Ne Bai Yi Imani Da Kaddara Ba!”

“Gobe Tafiyar da Baba Buhari Zai Yi Lagos Bikin Kaddamar Da Littafi. Allah Ya Dawo Mana Dashi Gida Arewa Lafiya”

“Yan Nigeria Minene Amfani Kiyayya Da Buhari Don Allah?”

“La’akari’ ‘Da ‘Yanda Shugaban Kasarmu Buhari Ya Fatattakar Cin “Hanci ‘Da Rashawa Nigeria A Cikin Shekaru 6 Kacal.
Mu Kam Zamu ‘Iya Cewa Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu!. Alhamdulillah

“Allah Ya Sa Buhari Ya Zama Jagoranmu Na Shiga Aljanna!

Allah Yasa Jami’an Tsaro Su Wargaza Duk Wata Zanga-Zanga Da Yan Nigeria Suka Shirya Yiwa Buhari

Kwatsam kuma a safiyar yau sai ga Surajo ya rubuta…

“Cikin Juyayi ‘Da Bakinciki ‘Nake Sanarda ‘Yan Uwana Musulmi.
A Garinmu ‘Na Kwasare Dake Wurno Local Gwamment Sokoto Cikin ‘Dare Jiya Wasu Marasa Tsoron Allah
Sunyi Awon Gaba ‘Da ‘Yan Uwan Haihuwata “Fiye ‘Da Biyar
INA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UON!”

Sai dai Muryoyi ta ruwaito nan da nan sai ga mutane sama da Dubu sunyi masa martani wato comment amma fa marasa dadi, domin kadan daga cikin comment da muka dauko:-

“INSHA ALLAHU SAURA KAI ZAKA SHIGA MASIFAR DA BAKA TABA TUNANINTA BA .

KUMA SU DA AKA KWASHE SU INDA BABARKA A CIKINSU SAI ANYI MATA FYADE KACHA KACHA SAN NAN SU JEFAR DA ITA ALLAH YA WADARANKA – inji wani Usman S Adam

“Kaje ka Jagoranci DSS kubi hanyar da suka bi ku nemo su amma naso ace Kai aka sace” –inji wani Ibrahim Umar

“Uban giji Allah yazama gatansu kai kuma Allah yasa su daukeka Dan darajar Annabi Muhammad saw” inji wani -Dan Asabe Westman

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: