Yan gani kasheni sun gargadi Bello Yabo ya daina sukar Buhari ko su saka kafar wando daya dashi

Daga Muryoyi

A wani mataki na rufe masa baki ko ta halin kaka, an gargadi babban malamin Addinin Islama na garin Sokoto, Sheikh Bello Yabo da ya daina fadin abubuwan da yake fadi game da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma masoyan shugaban kasar su saka kafar wando daya dashi.

Muryoyi ta ruwaito wani dan gani kashenin Buhari Muhammad Shehu ne ya fitar da gargadin a shafinsa na Facebook inda yake cewa basa jin dadin abubuwan da shehin Malamin ke fadi kan Gwamnatin Buhari “Jama’a ku shaida.. In dai Bello Yabo bai daina ba mu yan Buhariyya zamu sa kafar wando daya da shi” a cewar Muhammad Shehu

- Advertisement -

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: