Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYan Kaduna sun ji jiki, Zan dawo a 2023 —Inji Ramalan Yero

Yan Kaduna sun ji jiki, Zan dawo a 2023 —Inji Ramalan Yero

Daga Muryoyi

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramadan Yero ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2023 domin karasa ayyukan cigaban jihar da ya fara kafin saukarsa

Muryoyi ta ruwaito Yero na bayyana cewa ko a yanzu aka tsaya ya tabbatar jama’a sun fayyace bambancin mulkin PDP na shekaru 16 da kuma mulkin APC a shekara 8 kacal,

A cewarsa jama’a sun ji jiki a mulkin APC, sun rasa dukiyoyinsu, sun rasa muhallansu, sun rasa kasuwancinsu sun rasa matsugunnansu ga kuma uwa uba rashin tsaro da ya addabi jama’a har tsoron zuwa jahar Kaduna suke yi.

- Advertisement -

Tsohon Gwamnan ya cigaba da cewa yan jahar Kaduna nada sauran dama itace su zabe shi a 2023 domin da tsohuwar Zuma ake yin magani “shi yasan kalubalen da jahar ke fuskanta domin ya rike Gwamna kuma bai manta da komi ba, don haka zai fi cancanta ya dawo kujerar Gwamna domin ya bunkasa jahar Kaduna”

“Zan bunkasa jahar Kaduna ta yadda ya’ya da jikoki zasuyi alfahari da ita”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: