Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYan sanda sun kama wani mutum da ake zargi ya lakadawa Mai...

Yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi ya lakadawa Mai Sigari duka ya mutu akan N50

Daga Muryoyi

Rundunar yan sanda ta jahar ogun, ta kama wani mutum Dan shekara talatin da biyar, Biodun Adeniyi ranar litinin akan lakadawa wani mai sayar da cigari duka har lahira bayan ce-ce kuce da sukayi akan Naira Hamsin.

Wakilin Muryoyi ya ruwaito daga majiya mai tushe cewa mai magana da yawun yansandan ta Jahar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi ya sanarwa yan jaridu haka a Ota dake jihar Ogun.

ASP Abimbola ya bayyana cewa wanda ake zargin mazaunin Oladun Ikotun ne, kuma an kama shine a ranar 5 ga watan Disamba bayan Mahaifin wanda ya kashe ya kai rahoton ofishin yan sanda na Idiroko,

- Advertisement -

Oyeyemi ya bada bayani cewa binciken da sukayi ya nuna Adeniyi ya sayi Sigari da misalin karfe 2 na rana a wajen dansa dake tsaron shagon a lokacin, Mukaila Adamu, a shagonsa dake garin Ajegunle area, Idiroko,

Ya ce sai kuma ya dawo da wajajen misalin karfe 10 na daren ranar ya nemi a bashi canjin N50 lamarin da ya jawo masu hayaniya har ta kai ga ya rufe mai tsaron shagon da duka,

Muryoyi ta ruwaito nan take yaron ya zube kuma bayan an kai shi asibiti likitoci suka bayyana cewa ya rasu.

Shugaban yan sanda na Idiroko, CSP Shadrach Oriloye, ya yi gaggawar kai dauki wajen da abin ya faru inda suka samu nasarar kama wanda ake zargin tare da tura gawar mamacin zuwa dakin gwaji domin tabbatar da makasudin rasuwarsa

Kawo yanzu dai Kwamishinan yan sanda na jiharLagos, Lanre Bankole, ya umurci a tura wanda ake zargin zuwa babban sashin binciken manyan laifuka

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: