Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYunwa na neman kashe Nnamdi Kanu a kurkuku --a cewar lauyansa

Yunwa na neman kashe Nnamdi Kanu a kurkuku –a cewar lauyansa

Daga Muryoyi

Lauyan shugaban yan ta’addan IPOB masu fafutikar kafa kasar Biyafara Ifeanyi Ejiofor, ya zargi hukumar DSS da rashin kula da Nnamdi Kanu a kurkuku da suke tsare dashi, baya ga bakar wahala da suke bashi sannan kuma sun yi watsi da duk sharuddan da kotu ta basu,

A ranar 2 ga watan Disamba 2021 ne dai Alkalin kotu mai shara’a Justice Binta Nyako ta kotun daukaka kara ta tarayya ta shar’anta wasu dokoki na sassauci ga shugaban yan ta’addan.

Muryoyi ta ruwaito Ejiofor ne cewa a ziyarar da ya kai wa wanda yake karewa ranar 7 ga watan Disamba ya tarar yunwa na neman kashe shi, kuma Nnamdi Kanu ya gaya masa yana jin jiki a kurkukun.

- Advertisement -

Bugu da kari in ji shi rabonsa da abinci tun jiya (lahadi zuwa Litinin), sannan ya ce Nnamdi ya fada masa babu ko abu daya cikin hukuncin Kotu da DSS din suka aiwatar,

“Har yanzu Nnamdi Kanu ba mai laifi bane a dokar kasa, har sai kotu ta yanke hukunci don haka a yanzu zarginsa ake yi, idan kuwa haka ne yana da cikakken yanci kamar kowane dan Nigeria” a cewar lauyan nasa, daga karshe ya nemi DSS din suyi abunda ya dace ko kuma ya koma ya sanar da kotu

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: