Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuZanga-zanga ta barke a majalisar dokoki kan sai an tsige Ganduje

Zanga-zanga ta barke a majalisar dokoki kan sai an tsige Ganduje

Daga Muryoyi

A wani sabon yunkuri kuma, An fara zanga-zanga a zauren majalisar dokoki domin tursasawa majalisar dokoki ta jihar Kano tsige Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje bisa zargin cin hanci da badakala da dukiyar al’umma.

Muryoyi ta ruwaito wasu gamayyar kungiyoyi dake yaki da cin hanci da rashawa ne suka soma sabon yunkurin.

A sanarwar da matasan suka fitar a yau Juma’a sun yi kira ga duk wani mai rajin yaƙi da cin hanci da rashawa da ya ankarar da ƴan majalisar dokokin jihar Kano, da su fara shirye-shiryen tsige Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga kujerar Gwamna.

- Advertisement -

A cewarsu al’umma ta damu ƙwarai da gaske akan yadda aka mayar da Gwamnatin Kano mallakin wani mutum shi da iyalinsa, a karon farko a tarihin jihar Kano, an samu gwamnan da ya tsoma iyalinsa cikin harkokin gwamnati kuma su ke cin karensu babu babbaka.

Sanarwar ta yi zargin cewa yau a Kano an wayi gari cewa duk wanda iyalin Gwamna ke so to babu shakka kai tsaye za a azurta shi da dukiyar al’umma, wanda hakan ya saɓa da doka da kundin tsarin mulkin Najeriya.

A cewar masu zanga-zangar abun ya munana har ta kai ga an fitar da faifan bidiyo dake ikirarin nuna Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar wasu daloli da ake zargin cin hanci ne yana sankamawa a aljihhun babbar riga wanda hakan babban laifi ne ga tanadin doka.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: