Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuZulum yace ba zasu hukunta tubabbun yan Boko Haram ba saboda wasu...

Zulum yace ba zasu hukunta tubabbun yan Boko Haram ba saboda wasu dalilai

Daga Muryoyi

Gwamna Babagana Ummara Zulum na Jahar Borno ya yanke hukuncin cewa ba za’a gurfanar da tubabbun yan Boko Haram ba. Gwamnan ya fadi hakan ne a yayin gabatar da daftarin kasafin kudi na 2022 a zauren majalisar jahar ranar Talata.

Muryoyi ta ruwaito Gwamnan na cewa “Mai girma kakakin majalisa da sauran mambobi muna bukatan taimakon Allah matuka da hikima don ganin an kawo karshen tashe tashen hankula da yake damun jaharnam tamu” Ya Kara da cewa gurfanar da yan ta’addan da masu tada kayar baya zaifi dacewa amma idan muka dage akan hakan zamu hana wadanda suke ashirye su ajiye makamansu”

Sai dai Zulum ya yi kira ga yan ta’addan da su daina cigaba da kai hare-hare da kashe jama’a su zaci cewa idan sun zo sun tuba za a barsu “ba kuma shikenan zamu rika barin kowane dan ta’adda yana kashe jama’a da salwantar da dukiyoyinsu sannan yazo da rana tsaka yace ya tuba a kyale shi ba”

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: