Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAbunda yasa A.A Zaura ya sha gaban sauran yan takarar Gwamnan Kano...

Abunda yasa A.A Zaura ya sha gaban sauran yan takarar Gwamnan Kano 2023

Abunda yasa A.A Zaura ya sha gaban sauran yan takarar Gwamnan Kano 2023

A haƙiƙanin gaskiya, mu na da yalwatacciyar albarkar kasancewa kamar kowacce irin ƙasa da ta cigaba a duniya inda martaba, kykkyawar manufa da buri gami da sahihin tsari, shirin ilimi, da himma, da ƙulli da kuma yi da gaske gami da sadaukarwa ga al’umma da ƙanƙan da kai, da haziƙanci na haƙiƙa kan samar da sauyi shi ne ma’auni kuma babban abin duba na zaɓen shugaba, sannan zan faɗa da babbar murya ba tare da wata shakka ko kokwanto ba, mutumin da zai samu tikitin zama ɗan takarar jam’iyya a Jiharmu batare da wata taƙaddama ko kaiwa ga zaɓen fidda gwani ba.

Cikin girmamawa dangane da batun cancanta da iyawa ga wanda ya fi dacewa da cancantar samun babbar damar hawa kujerar lamba ɗaya, mu fahimci gaskiya mu fidda abin da ke ranmu babu nuƙu-nuƙu batare da son kai da ganin ido ba ko makahuwar soyayya ba ko biyan buƙatar kai ba, mu kalli bayanan shaidar duk ƴan siyasar masu neman kujerar mu ɗora su a sikelin awu mu gwada nauyinsu da wanda ya fi kowa cantanta, mai bincike mai nazari, ba shakka daga ƙarshe za mu fito da gaskiya cewa A.A Zaura shi ne a samansu gaba ɗaya.

Mutum ne wanda ya cika dukkan waɗansu sharuɗa. Mutum ne mai nagarta tun asali. Tsohon ɗan kasuwa wanda ya ke da damar zama shugaba ya tafikar cikin nasara duba da irin ɗumbin albarkar kasuwanci da ya samu a duk duniya. Kasuwancinsa ya na tafiya a bisa doron gaskiya da adalci da martaba a duk wani nau’in kasuwanci da zai yi, wanda wannan shi ne sinadarin da ya ɗaga tauraruwarsa zuwa matsayi na sama ya kasance ana irgawa da shi a cikin manyan mashahuran ƴan kasuwa masu nasara a duniya. A matsayinsa na wanda ya ga jiya ya ke ganin yau da kykkyawar ƙwaƙwalwarsa da zurfin tunaninsa idan ya samu nasarar zama gwamna zai yalwata hanyoyin tattalin arziƙin Jihar nan ya kuma samar da tsayayyen tsarin tattalin arziƙi mai yalwa mai ɗorewa daidai da tsarin ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arziƙi. Sannan zai kawo tsari mai kyau akan harkar haraji tayadda za a daƙile ƙofar da wasu su ke amfani da shi wajen azurta kansu a madadin yi wa jiha aiki.

- Advertisement -

Buɗaɗɗen abu ne a bayyane cewa siyasar Jihar a kowane lokaci cike take da rashin dattako da ƙazamin wasa a tsakanin ƴan jam’iyya ɗaya, da abokan hamayya. Yaɗuwar cin zarafi, ɓata suna, keta alfarmar ɗan adam, rashin ɗa’a da zarge-zarge marasa tushe, da sauran maganganun ɓatanci.

Mabiya su na kan kare waɗanda su ke ɗaukan nauyinsu, sun himmatu wajen yaƙi da aikata abin kunya kan ayyukansu na rashin ladabi, wannan mutumi A.A Zaura, ya wayar da kan mabiyansa, da masu taimaka masa kan kafafen sadarwa ya kuma hore su akan sanya ɗa’a da mutuntaka cikin ayyukansu, da tafikar da siyasa cikin girma da arziƙi da mutunta kowa. Su na yaɗa soyayya da zaman lafiya da aminci kan kiyaye doka da oda, su girmama doka da ƙa’ida ba wai su bi shi a makance ba. Ba za ka taɓa ganin wani daga cikin mabiyansa ya na ɓatanci da cin zarafin wani ba. A wurinsa siyasa hanya ce ta neman haɗin kan al’umma su mara baya a hau matsayi domin kyautata rayuwarsu. Ba wai harka ce ta a mutu ko a yi rai ba, duk wanda ya ke da gaskiya da himmar taimakon al’umma, ba wai wanda ya ke da tunanin ya samu matsayi domin kansa ba.

Mutum mai ilimi, wanda ya yi shuhura ya ke da yunwar karatu ya ƙwanƙwaɗi ilimi ya yi karatu ya samu horo da takardar shaida a fannoni daban-daban ya kuma yi digirin digirgir. Ya san darajar ilimi da amfaninsa ga al’umma, wannan mutumin har yanzu ya na kashe kuɗaɗe akan harkar ilimi inda ya ke gina ajujuwa da zuba kayan aiki, da ba da tallafin karatu ga ɗalibai marasa ƙarfi da gina makarantun islamiyya da kuma sabunta waɗanda ake da su, da sauran ayyuka da dama na agaji a fannin ilimi da sauran fannonin cigaban rayuwar al’umma wanda ya daɗe ya na yi tsawon shekaru.

Duba da kundin tarihi, duk waɗanda su ke neman wannan kujera a yanzu, to a baya sun taɓa riƙewa ko kuma su na riƙe da wani madafun iko a yanzu. Amma kuma duk ayyukan jinƙan al’umma da ya jima ya na yi wanda duniya ta shaida, gidauniyar A.A Zaura wanda ayyukan nata ya ratsa ko’ina har can ƙasan-ƙasa cikin al’umma mabuƙata ya kashe biliyoyin kuɗaɗe waɗanda ba za su lissafu ba.

Duk da haka shi ɗin ba zaɓaɓɓe ba ne, hasali ma bai taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba. Bai taɓa aikin gwamnati ba a kowane mataki. Shi ɗin ba kowa ba ne face ɗan kasuwa mai nasara wanda ya ke faɗi tashi wajen neman nakansa. Daɗi da ƙari, ba shi damar zama gwamna, zai samar da tsaro da aminci cikin gwamnatinsa batare da wata tangarɗa ba. Babu wani zargi da waɗansu tuhume-tuhume da za su faru. Ƙwarewarsa da ilimin da ya samu a tafiye-tafiye da hulɗa da manyan ƴan siyasa da manyan ƴan kasuwa a duk duniya ba shakka za su kasace an yi amfani da su wajen gina Jihar a kowane fanni na cigaban rayuwar al’umma daidai da yadda duniya ta ke tafiya tare da fasahar zamani. A matsayin ƙwararre kan harkar kasuwanci ta duniya ba shakka shi ne zaɓi mafi alkhairi wanda zai zo da abubuwa na zahiri da ke faruwa a duniya.

Yanayinsa na kasancewa matashi ƙari ne akan muradinsa na samar da cigaba tsarin da duk duniya ta runguma ta ke kuma tafiya a kai inda ta amince matasa su ja ta zuwa ga matakin cigaba na mafarkin da ake da shi. A taƙaice kamar tsarin da gwamnatin ƙasarmu ta samar na ba wa matasa dama, “Not too young to rule”. A Abdulsalam Abdulkareem Zaura, mun yi dace da albarkar samun matashi wanda ya ke ɗauke da manyan nauye-nauye a kafaɗunsa. Matashin da ya ke ƙona kansa da shiga halin yunwa domin ya taimaki al’umma. shirin samar da sabbin tsare-tsare, sauya hanyar da mu ke yin abubuwa, ƙirƙiro da albarkatu masu ɗorewa da yin komai a buɗe cikin gaskiya da adalci da daidaito wajen tafikar da gwamnati. Haƙiƙa ya cancanci samun goyon baya domin samar da kykkyawar gobe ga ƴan baya masu tasowa.

Daɗi da ƙari mutum ne mai kaifin hikima da hangen nesa wanda ya zama ƙwararre kan hasashensa da abin da zai yi. Abokan takararsa duk ba su da nasara a kansa saboda ya yi musu nisa kan abubuwan alkhairi, a kullum cikin hidimar ayyukan jin ƙai ya ke na ba da jari ga matasa domin dogaro da kai. Ya zuba kuɗaɗe masu yawa ya ɗauki nauyin mutane masu yawa inda yanzu haka su na nan su na zagayawa ƙananan hukumomi 44 na Jihar su na wayar da kan al’umma kan muhimmancin yin katin zaɓe. Aikin da ya kamata duk ƴan siyasa masu neman matsayi su yi koyi da shi. Ka da su manta da cewa zaɓe ɓata lokaci ne idan masu zaɓe ba su da katin zaɓe. Ya na da matuƙar tasiri a ba da muhimmanci matuƙa wajen wayar da kan jama’a muhimmancin yankar katin zaɓe. Kuma a gaskiya yanzu mu na zamani ne na yi Online jama’armu su na buƙatar ilimin hakan sosai da kuma tallafin da zai taimaka musu, akwai matsala idan har mu ka gaza wayar da kan jama’armu su yanki katin.

Ko da a tsare-tsaren ƙasa, ƙarfinmu shi ne yawanmu. Wannan yawan zai zama marar amfani idan har mutanenmu ba su yanki katin zaɓe ba. Wannan shi ne abin da ya zama lallai shugabanninmu su runguma, amma da dama sun gaza ba da cikakkiyar kulawa da goyon baya a kai. Amma shi A.A Zaura ya fahimta ya kuma maida hankali akai ya na kashe manyan kuɗaɗe a wannan fanni wanda daga ƙarshe ba shakka za ta amfani ƴan takara masu neman kowane irin matsayi.

Ba zan kammala batare da na bayyana cewa A.A Zaura ba wai albarka ba ne ga iya Jihar Kano ba, albarka ne ga ƙasa gaba ɗaya da ma jam’iyyu gaba ɗaya. Ga waɗanda ake wayar wa da kai ba wai iya wayar da kan ba ne, har da ɗan tallafin kuɗaɗe da ake ba su wanda zai sauƙaƙa musu wahalhalu wajen zuwa yin katin zaɓen. Kuma ana yi musu hakan ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba.

Kowacce Jiha a duk ƙasa za ta yi addu’a da fata gami da mafarkin samun irin wannan nagartaccen mutum a inda su ke. Mu dai Jiharmu mun yi dace da samun albarkar wannan zaƙaƙurin matashi ɗan asali, za mu yi duk wani abu mai iyuwa wajen tabbatar da cewa daga ƙarshe ya samu nasarar samun wannan kujera domin amfanin al’ummarmu.

DAGA Shariff Aminu Ahlan
Babban amintaccen mayaƙin Zaura.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: