Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAdamawa: Magidanci ya kashe matarsa mai ya'ya 8 bayan ya sake ta

Adamawa: Magidanci ya kashe matarsa mai ya’ya 8 bayan ya sake ta

Daga Muryoyi

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama wani magidanci mai sana’ar tukin mota dan shekara 57, Muhammed Alfa bisa zargin kashe matarsa mai shekara 40, Hamsatu Muhammad sakamakon daba mata wuka bayan ya sake ta ta je kwashe kaya.

Muryoyi ta ruwaito Kakakin rundunar yan sandan jihar DSP Suleiman Nguroje, yace lamarin ya faru a jiya Asabar a kauyen Lande B dake karamar hukumar Gombi,

Hamsatu wacce suke da ‘ya’ya 8 a tsakaninsu sun samu sabani har ta kai ga saki. Bayan mutuwar auren nasu ne sai matar ta kwashe kayan ta ta koma makota amma kuma sai rikici ya kaure a tsakaninsu lokacinda ta zo ta cire kyauren dakin ta zata saka a sabon dakin ta da ta samu a makwafta.

- Advertisement -

Wannan abu ya jawo cece-kuce har zuciya ta dibi magidanci Muhammed Alfa ya soka mata wuka a wuya, Muryoyi ta ruwaito nan take margayiyar ta fadi sume jini nata zuba kuma kafin a kaita asibiti rai yayi halinsa.

DSP Suleiman yace suna cigaba da gudanar da bincike domin gurfana da wanda ake zargin

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: