Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAlhaji Bashir Tofa: Ba Rabo da Gwani ba....

Alhaji Bashir Tofa: Ba Rabo da Gwani ba….

Rubutawa: Fatuhu Mustapha

Ku mu taro mu zabi NRC don kadda mu kai ga tabewa….

Na fara gamuwa da Alhaji Bashir Usman Tofa, tun zamanin NRC da SDP. Amma sani na mutum da mutum sai yan shekarun nan, sai dai cikin kankanin lokaci muka saba, ta zama kamar sanayyar shekara da shekaru.

A sanin da na yi masa, mutum ne mai dattako, da yakana, kishi da mutunta mutane. Baya shayin fadar gaskiya ko akan waye. Ga biyayya ga nagaba, domin ni shaida ne akan wannnan. Ya taba gaya min dalilin da ya hana shi fito da biography din sa, ya ce min saboda wasu manya da yake ganin girman su sun hana shi. Da na ce masa ai duk sun rasu, sai ya ce min, in har bayan rasuwar su zan saba musu, to ban ga dalilin da zai sa in ki yi a gaban idon su ba. Ya kara da cewa ba tarbiyar mu ba ce, kin biyayya ga maganar na gaba. Anan na dauki wani sabon darasi na rayuwa. Wani abin shaawa game da shi shi ne, duk da nacin da nayi tayi masa akan littafin, amma bai taba nuna bacin rai akan na dame shi ba, ko a waya ko gaba da gaba, abinda dai yake gaya min, ba zai haura umarnin da manyan sa suka ba shi ba.

- Advertisement -

Alhaji Bashir mutum ne karimi, domin ko a yau daya daga cikin abokan sa na kusa, Malam Bilya Bala, ya bamu labarin daya daga cikin irin karimcin sa, in da ya ce mana karshen ganin sa da shi, watannin baya sun hadu domin su hada kudi su taimakawa wani abokin su, sai Alhaji Bashir ya ce, shi duk abinda aka tara, sai bayar da linkin biyu, haka kuwa aka yi. A lokacin da ya dauki studio din Arewa House gaba daya ya bayar ga wasu mawaka, na tambaye shi cewa, baya ganin na za su yi amfani da shi yadda ya dace ba? Sai ya ce min, mu dai mun yi abin da ya dace a matsayin mu na iyaye, saura kuma ya rage nasu, su baiwa mara da kunya.

Mutum ne mai zurfin tunani da fikirar magana, zama na da shi na fahimci rayuwa nayi karatun rayuwa kwarai a wurin sa. Mun tattauna akan ilmin taurari, yadda ake rubutun zube, alakar su da IBB, abinda ya hada su da Abacha, yadda rikicin na su ya zamar masa alheri, har ya rubuta tarihin musulunci, da makomar Arewa bayan mulkin Buhari, da yadda ya zama Shugaban Jam’iyyar NPN yana yaro matashi kai har da alakar sa da babban abokin sa, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi. Anan na lura da cewa, banbancin aqida ko fahimta, bai sa ka bata da abokin ka. Domin a lokacin da suka dawo daga karatu a gidan sa Rimi ya zauna, amma sai ga Rimi yana PRP shi kuma yana NPN, kuma hakan bai taba shafar abokantakar su ba, duk kuwa da dagar da aka shaya a tsakanin jam’iyyun guda biyu. Ya kuma sha min nasihohi da suka haska min hanya.

Alhaji Bashir, mutum ne mai barkwanci da haba haba, zai wuya ka same shi, kuyi hira baka fito cikin farinciki ba. Duk saurin da kake in kuka fara hira da shi, sai ka manta abinda ke gabanka. Ya taba bani wani labari na yadda suka sanya J S Tarka a jirgi daga Lagos zuwa Kano, labari ne mai ban dariya. Da yadda suka fafata da Hassan Sarkin Dogarai a gaban sarkin Kano Ado, har suka sa Sarki dariya a fada. Da wasu labarai masu ban dariya da naji a wurin sa. Musamman haduwar su da wani attajiri mutumin Kano a Brussels. Wani abun da bana mantawa kuma yake bani dariya a game da shi, shi ne yadda ya dage allankatafar ni abokin sa ne, ba da ba. Abin ya faru ne, da nayi masa waya na nemi izinin zan zo in gaishe shi, sai ya gayawa masu gadin gidan sa, cewa wani abokin sa zai zo. Wannan ya sanya da na zo, masu gadin suka ce su dai ya ce musu abokin sa zai zo, bai ce ni ba, amma in kira shi a waya. Da na kira shi, sai ya ce min ai ya gaya musu zan zo, na ce masa su dai sun ce abokin ka zai zo. Sai ga shi ya fito yana musu fada, ba yace musu abokin sa zai zo ba. Nan aka bar ni da baki a wangale ina kallon ikon Allah. Tun daga lokacin muke wannan mahawara da shi, shi ya dage akan ni abokin sa ne, nake zuwa mu yi hira, ni kuma na dage dan sa ne nake zuwa in karu da ilmin da Allah ya bashi. Magana ta ta karshe da shi, kusan yan satuttukan baya ne, da na kira in gaida shi, yake ce min baka kawo yaranka ba da ka ce suna so su zo su gaida ni. Saboda na gaya masa mun wuce ta kofar gidan da su, suna tambayar gidan waye, na ce zan kawo ku gaida shi, wani kakan ku ne.

Rayuwar Alhaji Bashir Tofa darasi ce ga matasa, su fahimci cewa ba tarin shekaru bane nasarar rayuwa, ilmin da biyayya ga nagaba da kuma son jama’a ita ce nasarar rayuwa. Mutum ne mai kishin addinin sa, bai taba yadda da zalunci ba, dalilin da ya sa ya sha daga da shugabannin Nigeria da dama

A gaskiya Kano, Nigeria da mutanen Arewa mun yi rashin mutum mai kishin mu da son cigaban mu, zai wuya a mayar da kamar sa.

Allah ya jikan sa da gafara, ya yafe kurakuran sa, ya sa aljanna makoma.

Kaico! Ba rabo da gwani ba!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: