Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn hana KASTLEA binciken ababen hawa daga 8 zuwa 10 na safe...

An hana KASTLEA binciken ababen hawa daga 8 zuwa 10 na safe don saukakawa dalibai da ma’aikata

Daga Muryoyi

Daga yanzu hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kaduna, KASTLEA ta haramtawa jami’an ta binciken ababen hawa daga karfe 8 na safe zuwa karfe 10 na safiyar kowace rana.

Mutane, masu zuwa makaranta, ma’aikata da sauransu na korafin ana takura masu da bincike a lokacinda suke hanzarin zuwa ma’aikata ko harkallolinsu amma yanzu wannan doka zai saukaka masu isa akan lokaci.

A wata sanarwa da shugaban ayyuka na KASTLEA, Comrade Aliyu Manga ya fitar ya ce daga yanzu jami’an zasu rika ayyukan kiyaye cinkoso ne a wadannan lokuta “amma ba batun tsaida wani ko yi masa tambayoyi” inji sanarwar

- Advertisement -

Muryoyi ta tuntubi wani jami’in KASTLEA domin karin bayani kan wannan doka da aka sanya masu. “An saka dokar ne saboda ma’aikata na korafi cewa Jami’an KASTLEA na takura musu suna hana su zuwa aiki akan lokaci. Abun ya zama harda sheri domin sai ma’aikaci yayi zamansa a gida idan aka tuhumeshi sai ya fake da cewa KASTLEA ne suka hana shi”

“Saboda haka a yanzu babu wannan. Daga karfe 8 zuwa 10 na safe yan KASTLEA ba zasu tsaida ababen hawa da sunan bincike ba sai dai su tabbatar an kiyaye dokokin hanya sannan sun kawar da duk wani cinkoso inyaso daga karfe 10 na safe zuwa sama ana iya binciken ababen hawa”

Wannan mataki dai yayi ma masu ababen hawa dadi ganin cewa mutum zai iya yin harkokinsa na yau da kullum, kasuwanci, ko masu zuwa makarantu daga karfe 8 zuwa 10 ba tare da fargaban tsaida shi ko bincikensa ba.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: