An kama matar Aure dake zuwa wajen dan bindiga yana lalata da ita ya bata dubu Biyar

Daga Muryoyi

Wata matar aure da aka kama tana zuwa wajen wani dan bindiga yana lalata da ita ta ce gudun kada a kashe iyayenta ne yasa take zuwa ta bashi kanta.

Muryoyi ta ruwaito matar wacce ta shiga hannun jami’an tsaro ta ce tunda take zuwa wajensa yana lalata da ita sau daya ya taba bata Naira 5,000.

Bincike ya nuna matar na zaune ne a kauyen Tankarau a yankin Madaci da ke Karamar Hukumar Zaria ta Jihar Kaduna.

- Advertisement -

A cewar ta sunan dan bindigar da take zuwa wurinshi yana lalata da ita Idi Dan Ibrahim.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: