Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBashir Tofa ya bar wasiyyar kada ayi masa zaman makoki da kuma...

Bashir Tofa ya bar wasiyyar kada ayi masa zaman makoki da kuma…

Daga Muryoyi

Bashir Tofa ya bar wasiyyar kada ayi masa zaman makoki da kuma inda yake so a bizne shi da wanda zai

Muryoyi ta ruwaito cewa Iyalan margayi Alhaji Bashir Tofa da ya rasu dazu sun sanar da mutanen da suka halarci jana’izar marigayin bayan dawowarsu daga maƙabarta cewa ya bar wasiyyar kada a yi masa zaman makoki.

A tattaunawar wasu makusanta da makofcin mamacin sun shaidawa Muryoyi cewa sauran wasiyyoyin da mamacin ya bari sun hada da inda za a bizne shi, da limamin da zai yi masa sallah da kuma inda za ayi masa sallah.

- Advertisement -

Alhaji Ahmad ya gaya mana cewa Mamacin ya bar wasiyyar a bizne shi a makabartar Hajj Camp, kuma anan din aka bizne shi a tsakiyar kabarin mahaifinsa da mahaifiyarsa.

Sannan ya bar wasiyyar Sayyadi Bashir Tijjani Usman yayi masa sallah kuma hakan akayi.

Muryoyi ta ruwaito Alhaji Bashir Othman Tofa ya kuma bar wasiyyar ayi masa sallah a kofar masallacinsa a cikin gidansa kuma hakan akayi.

“Dayake shi mutum ne mai aiki da lokaci ya nemi don Allah a gaggauta yi masa sallah idan ya mutu wannan yasa tun wajen karfe 9 na safe aka sallaci gawarsa ba tare da jinkiri ba” inji wani makwafcinsa

A dazu ne dai Muryoyi ta ruwaito maku labarin rasuwar attajirin dan kasuwa kana dan siyasa Alhaji Bashir Othman Tofa wanda ya rasu yana da shekara 74 kuma ya rasu ya bar mata daya Hajiya Hauwa da ‘ya’ya 6, Biyu maza 4 mata

Bashir Shu’aibu Jammaje ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Yayin dawowa daga jana’izar Alhaji Bashir Tofa. A lokacin da ake sanar da mutane cewa ba za a yi zaman makoki ba. Ya bar wasiyyar cewa kar a yi hakan. Shi ya sa ko tabarma ba a shimfiɗa ba, kowa ya yi gaisuwa sai ya tafi”.

Ya ce, “mun yi rashin Uba kuma Jagora. Akwai darasi ainun a rashin irin waɗannan manyan bayin Allah na gari.

Allah Ya jiƙanshi ya yafe mishi ya sa Aljanna Firdaus ce makomarshi, amin”.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: