Daga Muryoyi
Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafafen yada labarai Buhari Sallau ya gwangwaje daruruwan matasa da fantsama fantsaman wayoyin salula tukuici kan yadda suke ta dawainiya da APC da Gwamnatin Buhari
Mafi yawan matasan suna gudanar da ayyukan sana’o’i da wayar salula wanda hakan ya taba zuciyar hadimin shugaban kasar ya sayo masu wayoyi domin amfanin kansu da kuma neman kudi ta hanyoyin zamani na sadarwar zamani.
Muryoyi ta ruwaito a karon farko an raba wayoyi fiye da dari kuma ana sa ran dorawa a rukuni na gaba,
- Advertisement -
Malam Buhari Sallau ya lashi takobin cigaba da yin bakin kokarinsa wajen ganin matasa sun afamana da romon Dimokuradiyya musamman matasan da ke yayata ajendar APC da shugaba Buhari a kafofin sadarwar zamani
Matasan sun yi godiya sosai tare da nuna jin dadinsu bisa wannan sha tara na arziki