Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: El-Rufai ya rage ranakun zuwa makaranta a Kaduna, ya koma...

DA DUMI-DUMI: El-Rufai ya rage ranakun zuwa makaranta a Kaduna, ya koma Litinin zuwa Alhamis

Daga Muryoyi

Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci duka makarantun Gwamnati a fadin jihar Kaduna su koma bin sabon tsarin aiki na kwana hudu wato Litinin zuwa Alhamis.

Muryoyi ta ruwaito Kwamishinar ilimi ta jihar Kaduna, Halima Lawal, ta bayar da sanarwar hakan ga duka makarantun jihar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce a yayin da za a soma zangon karatu na Biyu wato Second term daga ranar Litinin 10 ga watan Janairu daga yanzu babu makaranta duk ranar Juma’a

- Advertisement -

Halima Lawal, ta kara da jan kunnen makarantu su kiyaye dokokin tsaro da na kiwon lafiya da aka tsara domin kare dalibai. Sannan ta bayar da lambar waya da za a kira a duk lokacinda ake zargin wani abu da ya shafi tsaro a makarantu ko harabar makarantu a jihar Kaduna 09034000060 ko 08170189999

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: