Daga Muryoyi
Gwamnatin Kaduna tace dokar hana acaba da yawo akan babur a fadin jihar Kaduna tana nan daram. An tsawaita dokar har sai yadda hali yayi.
Sauran dokokin da aka tsawaita sun hada da dokar hana yawo da Keke-napep daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe a kananan hukumomin Birnin Gwari, da Giwa, da Igabi, da Chikun, da Kachia, da Kagarko da kuma Kajuru
Muryoyi ta ruwaito Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan na cewa Gwamnan jihar ya baiwa jama’ar Kaduna hakuri bisa daukar wadannan tsauraran dokoki. Amma yace anyi ne domin tsare rayuka da dukiyoyin jama’a
- Advertisement -