Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEl-Rufai yace mafita shine a kona dazuka ayi wa yan bindiga ruwan...

El-Rufai yace mafita shine a kona dazuka ayi wa yan bindiga ruwan wuta ta sama da ƙasa

Daga Muryoyi

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai yace a nasa ganin ƙona dazukan arewa shine zai bayar da dama a ƙakkabe ɓarayin daji da suka addabi yankin.

El-Rufai a hirarsa da majiyar Muryoyi ya ce “Na sha faɗa cewa, abin da ya kamata shi ne a ƙona dajin, a kashe su gaba ɗaya, daga baya mu sake shuka bishiyoyi,”

A cewarsa ƙona dajin ne kawai mafita duk da matakin zai shafi waɗanda ba su ji ba su gani ba amma ya fi a kakkabe su a dawo da zaman lafiya mutane su koma noma,

- Advertisement -

Gwamnan na ganin yadda ake tunkararsu a yanzu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba – “domin idan an kore su daga Sokoto, za su tsere su tsallaka Kebbi.” don haka a cewar El-Rufai “Abin da za a yi kawai a yi masu ruwan wuta ta sama da ƙasa a dukkanin jihohi shida na arewa maso yammaci da Neja.”

Yace idan aka yi haka yana ganin cikin makwanni ana iya maganin matsalar gaba daya.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: