Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuIna da gogewa a siyasa zan iya maye gurbin Buhari a 2023...

Ina da gogewa a siyasa zan iya maye gurbin Buhari a 2023 kuma in dora daga inda ya tsaya –inji Bashir

Daga Muryoyi

Mai taimakawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labaru Bashir Ahmad ya bayyana cewa shi ɗan siyasa ne a yanzu, kuma damar aiki da ya samu a ƙarƙashin shugaban ƙasa tsawon shekaru 7 gami da mu’amala da manyan ƴan siyasa, ya samu gogewa da ƙwarewar sanin siyasa da dabarun mulki fiye ma da yadda wasu tsofin ƴan siyasar su ka sani.

 

Bashir dan kimanin shekara 30 wanda yayi digirinsa na farko a BUK kan harkokin sadarwa ya fito ne daga Gaya ta jahar Kano inda ya tsunduma harkokin siyasa tun yana shekara 24 bayan yayi Gwagwarmaya a kafofin sadarwar zamani a matsyin dan Jarida.

Mista Bashir ya kara da cewa a yanzu babu wani matsayi da zai yi masa girma ko da kuwa na shugaban kasa.

 

- Advertisement -

Hadimin shugaban kasar na bayani ne a jiya Lahadi, a ya yin tattaunawar kaitsaye da wata kafar yada labarai Arewa Media tayi dashi inda ya ce, “Ina da gogewa a siyasa, babu wani matsayi da zai mun girma a yanzu, ko shugaban ƙasa ƴan Nageriya su ka ce na fito zan fito kuma zan ɗora daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya”. Inji Bashir Ahmad.

 

Tunda farko cikin tattaunawar Bashir Ahmad ya bayyana irin nasarori da cigaban da ake samu a gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari musamman ta fuskar yaƙi da cin hanci da rashawa, bunƙasa tattalin arziƙi da kuma samar da tsaro.

 

“Idan mu ka yi duba da yankin Arewa maso Gabas an samu gagarumin cigaba da zaman lafiya tun bayan zuwan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015. Ko da matsalar da ake fuskanta yanzu haka a shiyar Arewa Maso Yamma rashin ayyana ƴan bindiga da ɓarayin daji a matsayin ƴan ta’adda shi ne ya haifar da tsaiko wajen gamawa da su saboda kare rayukan mutane marasa laifi, amma yanzu an ayyana su a matsayin ƴan ta’adda bisa doka kuma za a yi maganinsu”. Cewar Bashir Ahmad.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: