Daga Muryoyi
Mun samu labarin rasuwar attajirin dan kasuwa kuma dan siyasa dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NRC a 1993, Alhaji Bashir Othman Tofa.
Muryoyi ta ruwaito margayin ya rasu ne da sanyin safiyar yau Litinin a Asibitin koyarwa na Aminu Kano Teaching Hospital kamar yadda wani amininsa da makwafcinsa suka sanarwa Muryoyi a wayar tarho.
Tun a ranar Juma’a aka yada rade-radin cewa Bashir ya rasu amma daga bisani wani danginsa Ahmed Na’abba ya musanta labarin.
- Advertisement -
Muryoyi ta ruwaito an haifi margayi Bashir Othman Tofa a ranar 20 ga watan Yuni, 1947 ya rasu yana da shekara 74 a duniya.