Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKarfa-karfa akayi wa Kanawa a 2019 aka dora Ganduje --inji Kwankwaso

Karfa-karfa akayi wa Kanawa a 2019 aka dora Ganduje –inji Kwankwaso

Daga Muryoyi

Tsohon Gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso yace kowa ya sani a 2019 Abdullahi Ganduje ya fadi zabe jama’a sun fito karara sun nuna basa son shi amma wasu daga sama suka yi wa kanawa karfa-karfa suka dorashi akan mulki,

Kwankwaso yace amma dayake Allah mai sakayya ne sai gashi ba aje ko ina ba ‘duk sun dandana kudarsu’ yanzu kowa na nadamar yin haka ‘duk da cewa an riga an kwafsa’

“Ina tunanin wasu daga cikinsu na kokarin gyara kuskuren da sukayi bayan an gama kassara jihar, Abun takaici ne ace tun a 2019 wasu mutane suka kasa hango abunda talakawa suka hango suka ki zabarsa ba”

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Kwankwaso a tattaunawarsa da jaridar Punch ya yace a lokacin suna da damar daukar mataki ko kuma hana magudin amma dayake basu son a kassara jihar Kano sai suka bi hanyoyin da doka ta tanada kodayake anan din ma duk kanwar ja ce.

“Yanzu gashi mulki ya kawo karshe za a buga gangar siyasa shi kuma Ganduje zai ji da tulin kararrakin da aka maka shi a kotu” kuma wani abun jin dadi da godiya ga Allah shine, siyasar mu na ta kara karfi mutane na ta dawowa bangaren mu nasu bangaren kuma na ta dusashewa da kara rauni.

A cewar madugun Kwankwasiyya zaben 2023 ya sha bambam da sauran zabubbuka duk mai tunanin yin amfani da INEC ko jami’an tsaro ya murde zabe to ya sauya tunani tun da wuri domin yan Nigeria a shirye suke su canza canji.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: