Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKUKAN MAKASHIN HANEEFAH... Da minti daya bana tausayinsa

KUKAN MAKASHIN HANEEFAH… Da minti daya bana tausayinsa

Daga Auwal Garba Dan Borno

Ba yana kuka bane saboda nadamar abinda ya yiwa Haneefa. Ya na kuka ne domin yanayin da rayuwar sa ta shiga, da kuma hukuncin da zai fuskanta.
Wani abun lura. A lokacin da aka kama shi, jikinsa babu wata alama ta zullumi da rama da tashin hankali, duk Wanda ke tantama ya je ya duba hotonsa na farkon kamawa, da Interview na farko da Yan Jaridu su ka yi ma sa. Idan har kukan nan na yanzu nadama CE, kwanan sa na wa da kashe Yarinyar kafin a kama shi.

 

NIYYAR SA TUN FARKO.

Dama tun farko wannan niyyar ta kisan Haneefa na ransa. Yarinyar nan Dalibar sa CE, sannan Makasudin Kidnapping din shine wai Dan ya sami kudaden biyan Hayar Matsugunin Makarantar, da kuma sallamar Malamai. Kenan ya na da burin cigaba da zama, da kuma cigaba da tafiyar da Makarantar sa. Idan misali ya karbi kudaden kuma sai ya sake ta, Yarinyar za ta fadi ma Iyayenta Cewa Uncle wane ne ya dauke ni. Daga nan asiri zai tonu, zai shiga wannan halin da ya ke gudu Wanda ya shiga yanzu.

- Advertisement -

DA MINTI DAYA BA NA TAUSAYIN SA.

Lallai ana tausayawa Mummunar Kaddara ga duk Wanda ta same shi. Akwai Mummunar Kaddara da dole ka tausaya ma su. Misali kawai daga Cacar baki tsakanin wasu ko daga mari sai kawai Wanda aka Mara ya fadi ya rasu, wanda ya yi Marin ko da cikin fushi ne, bai da niyyar kashe Wanda ya Mara. Wannan dole ya zama abin tausayi saboda ba da niyyar ba ya yi kisa, kuma zai fuskanci hukunci.
Amma mutum ya dauke ‘Yar Mutane da niyyar Azurta kansa, ta yi kwana da kwanaki a wajen sa, bayan karbar kudi kuma ya kasheta da Shinkafar Bera. Wannan Dan Allah da wacce Zuciyar zaa ji tausayin sa. Kawai Dan an shiga Shafin sa na Facebook an ga rubutuka ma su kamar waazi waazi nasiha nasiha shikenan ya zama mutumin kirki.
Mutumin Kirki ba zai taba yin wannan abin na bushewar zuciya ba, sai in dama kura da fatar Rago ne, A zuci Fir’auna a Fuska Musa.

Ashe Shekau da kama shi aka yi sai an sami mai tausaya ma sa. Shin idan ka tausawa MAKASHIN Haneefa, ya za ka yi kuma da Iyayenta da Sauran ‘Yan uwanta, irin Kuncin halin da ya jefa Rayuwar su. Shin ma su Maganar tausayin nan su na da ‘ya’ya kuwa, ya za ka ji idan ‘yar ka aka dauke har aka ja ma rai na kwana da kwanki, aka karbi kudin ka sannan aka kashe ta.

Gaskiya wannan ya nuna muna cikin wata alummah da an fi ganin kimar mai aikata laifi kan Wanda ke kokarin tabbatar da adalci.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: