Daga Muryoyi
Dangi da ƴan uwan yarinyar nan Hanifa da ake zargin malaminta ya sace tare da kashe ta, kana ya binne gawarta a gidansa a jihar Kano na ci gaba da alhinin rasuwarta.
Cikin kuka da hawaye, mahaifin Hanifa, Malam Abubakar Abdussalam, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun shiga cikin mummunan tashin hankali sakamakon lamarin da ya faru, har ta kai ga an kwantar da mahaifiyar marigayiyar a asibiti.
‘Maganata ta ƙarshe da Hanifa’
- Advertisement -
”Magana ta ƙarshe da na yi da ita ce wadda na yi da ita ranar da za a sace ta, ta zo za ta tafi makaranta mahaifiyarta ta ce Hanifa ba ki yi addu’a ba, ta ce na yi, ta sake yi tana cewa ‘Bismillahi Tawakkalt Alallah’, tana yi da ƙarfi don ta ji cewa ta yi ɗin, ina ce mata to Hanifa kin yi, na yadda kin yi yanzu, ta tafi ta je tana sallama da mahaifiyarta, tana ce mata tun da za ki tafi kasuwa idan kin je ki taho min da alewar madara ina son zan yi sadaka da hannuna,” a cewar Malam Abubakar.
Ya ce lokacin da ya samu labarin an kama mutumin da ya sace ta ɗin ya ji daɗi, bisa tsammanin cewa zai nuna wurin da ya ɓoye ƴarsa, amma daga baya sai ya ji abun da ya saɓa da hakan.
Ya kuma shawarci iyaye su ƙara zage dantse wajen kula da ƴaƴansu, sannan a ci gaba da addu’ar Allah ya ba da zaman lafiya mai ɗorewa