Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMasu garkuwa sun kashe Hanifa bayan sun karbi Miliyan 6 kudin fansa

Masu garkuwa sun kashe Hanifa bayan sun karbi Miliyan 6 kudin fansa

Daga Muryoyi

Wadanda sukayi garkuwa da yarinyar nan yar shekara Biyar Hanifa Abubakar sun kashe ta bayan sun karbi kudin fansa har Naira miliyan shidda (N6M)

Kawun yarinyar Suraj Suleiman, ya ce masu garkuwan sun sanya mata guba a shayi bayan ta sha ta mutu sai suka sassara namanta kashi-kasho sannan suka bizne a harabar wata makaranta dake Tudunwada a jihar Kano

Muryoyi ta ruwaito daga majiya mai tushe cewa wanda yayi garkuwa da margayiyar ya kaiwa matarsa ta ajiye ta amma taki karbar ta daga nan ya yanke shawarar kashe ta.

- Advertisement -

An kama wadanda ake zargin ne bayan a hanyar Zaria zuwa Kano da yammacin jiya Laraba.

Muryoyi ta ruwaito an sace Hanifa ne tun a ranar 4 ga watan Disamba 2021 a hanyar ta na dawowa gida daga Islamiyya

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: