RA’AYI: Talaka Bawan Allah…

Rubutawa: Saifullahi Hassan Aikawa

A irin wannan mulkin da ake a Najeriya, babu wani shiri da akai dan talaka yaji dadin Damukuradiyya, duba da yana yin yadda kullin abubuwa su ke kara tabarbarewa misali, idan ka dauki harkar tsaro, zakaga cewa kullin illar rashin tsaron kasa a kan talaka take karewa, sakamakon shine bashi da gata, amma ga masu wakiltar talakawan sukan yi amfani da kudin talakawan wajen fitar da iyalin su kasashen ketare a Duk sanda matsalar tsaron ta taso, tamkar iya iyalin su kawai suke jagoranta. Kullu yau min zaka tashi daga barci ka sami labarin cewa an sace ka/dan talaka, an kashe dan talaka da shauran abubuwa makamanta haka, marasa dadin ji.

Idan ka dauki abin da ya shafi kayan amfani na yau da kullin, talaka baya cewa komai domin kuwa shi damuwarsa kawai shine ya samu wanda zai ci a kullin ba sai ya aje na sati ko wata guda ko ma shekara b, Kuma shi wannan talakan bashi da zabi, dan kuwa komai ya samu mai dadi ko Mara dadi haka zai karbe shi hannu biyu-biyu cikin murna da farin ciki yayi amfani da shi. Ammafa ga shuwagabannin, labarin ya sha banban, domin kuwa su kan aje abinci kala-kala harma da na banza, wani lokacin ma har ya lalace, ba magana ake ta tuwo ko shinkafa b. Magana ce ta shinkafa Basmati da shauran abubuwan more rayuwar da dani da kai ba lallai mun san sunan su ba balle muci, hadin mu da su sai dai ko a hoto kawai. Shin talaka ina zai kai kansa?

Wannan fa ba wani abu aka fada daga cikin abubuwan da ke addabar talaka b, kawai kadan daga cikin kadan ne aka tsakuro. Amma a haka talakan yace da zai samu a bashi iya tsaro ma kawai, shi zai ci gaba da fadi-tashi wajen samo dan abin da zai yi amfani da shi domin yayi magani wannan muguwar abar wato yunwa ya kuma rufa wa kansa asiri.

- Advertisement -

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: