Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuShaci faɗi Kwankwaso keyi don yaga ta kare mashi a siyasa --martanin...

Shaci faɗi Kwankwaso keyi don yaga ta kare mashi a siyasa –martanin Ganduje

Daga Muryoyi

Da alamu hirar da tsohon Gwamnan jihar Kano yayi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da jaridar Punch ya sake tada kura kuma bai yiwa Gwanatin Kano dadi ba har ta kai ga tayi martani.

A dazu ne dai Muryoyi ta ruwaito maku yadda Kwankwaso ya yi ikirarin cewa Ganduje bai ci zabe ba a 2019 kakabawa kanawa shi akayi kuma wadanda sukayi hakan Alhaki ya kama su wasun su kuma suna cike da danasani.

Sai dai a wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin jihar Kano mai ɗauke da sa hannun kwamishinan watsa labaran jihar Muhammadu Garba, ta bayyana kalaman na Kwankwaso a matsayin shaci faɗi da ko kaɗan ba bu ƙanshin gaskiya a cikinsu.

- Advertisement -

Abun takaici ne yadda a matsayin Kwankwaso na shugaba, wanda ake damawa da shi a harkokin gudanar da zaɓe ya kasa amincewa da sakamakon zaɓen da hukuma mai zaman kanta ta gudanar kuma kotu ta amince da shi” in ji Sanarwar.

Gwamnatin ta Kano ta ci gaba da cewa hirar da Kwankwason ya yi da jaridar Punch ta janyo masa mummunar illa ne fiye da alfanun da ya yi tsammanin za ta haifar masa.

A cewar ta a fili take cewa Kwankwaso ya fahimci gwamnatin Ganduje ta tsere wa sa’a wajen shimfiɗa muhimman ayyuka ga jama’a, shi ya sa yake ganin ana ƙoƙarin shafe abun da yake ganin ya yi a nasa

”Kwanan nan aka ji shi yaa jan hankalin magoya bayansa su kaucewa furta miyagun kalamai amma sai ga shi ya ɓige da yi shi da kansa, ko kaɗan wannan bai dace da shi ba”.

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: