Daga Muryoyi
Sanata Shehu Sani yasa an wallafa Al-Qur’ani, da Arba’una Hadith, da Rabbanah 40, da Allahummah 40, da Husnil Muslim, da kuma wani littafin addu’o’i ga mamata domin a raba ga makarantun Islamiyyoyi sadaka da niyyar Allah Yakai ladan ga marigayi Aminu Muhammad Maisalati.
Sannan kuma ya dauki nauyin karatun yayan shi har zuwa University kafin azo ga maganar muhalli.
Aminu mai salati babban magoyi bayan Shehu Sani ne kuma dan gani kasheninsa wanda Allah yayiwa rasuwa ranar 25 ga watan Disamba 2021.
- Advertisement -
Jama’a da dama sun yabawa Sanatan domin ba kasafai suke damuwa da magoya bayansu ba idan sun shiga wani hali musamman har ace ta kai ga mutuwa.