Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuTinubu yaje Villa ya nemi tabarrakin Buhari zai tsaya takara a 2023...

Tinubu yaje Villa ya nemi tabarrakin Buhari zai tsaya takara a 2023 domin dorawa daga inda Buhari ya tsaya

Daga Muryoyi

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa ta fitowa takarar shugabancin kasa a 2023,

Mista Tinubu ya ziyarci fadar shugaban kasa Buhari a yammacin yau Litinin kuma ya gana da shugaban kasar inda ya fada masa aniyar tasa sannan kuma ya nemi tabarakkainsa.

Muryoyi ta ruwaito Tinubu ya gayawa maneman labarai dake fadar shugaban kasa cewa makasudin ziyarar tasa shine sanarwa da shugaban kasa aniyarsa ta fitowa takara a karkashin jam’iyyar APC a babban zabe na 2023.

- Advertisement -

”Na shafe tsawon rayuwata ina mafarkin zama shugaban Najeriya, don haka ban yi tsammanin shugaba Buhari zai ce kar in yi takara ba” inji Tinubu

A cewar Tinubu Shuaban kasar yayi na’am da wannan mataki da ya dauka tare da yi masa fatan Alkhairi.

Jagoran APC kana tsohon Gwamnan Lagos din Tinubu ya ce yana da cikakken yakinin cewa yana da hangen nesa, da kudurori, da manufofi da gogewar da zai dora daga inda Buhari ya tsaya idan ya gaji Buhari a 2023.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: