Daga Muryoyi
Muryoyi ta ruwaito Jagoran jam’iyyar APC mai neman takarar shugabancin kasa a 2023 Bola Ahmed Tinubu yace yana goyon bayan muradin matasan Najeriya na neman matashi ya zama shugaban kasa amma su dakata sai bayan Tinubu fara zama shugaban kasa ya sauka su karba
Tinubu yayi wannan bayani ne a lokacinda ya ziyarci fadar basaraken Oyo wato Alaafin a yau Lahadi
Muryoyi ta ruwaito Tinubu na cewa “Ina rokon Allah yayi maku albarka yaku matasa ku girma ku zama dattawa kamar mu. Ku ma zaku shugabanci Najeriya amma kafin nan sai nayi nawa shugabancin na kammala sai kuyi naku….”
- Advertisement -
Mista Tinubu dai ya je Ibadan ne domin kai ziyara ga sarakunan gargajiyan jihar musamman sabon basaraken Ibadan wato Olubadan of Ibadanland.
Takarar Bola Ahmed Tinubu na shan suka saboda yadda ake ganin ya tsufa kuma matasa na ganin lokaci yayi da zasu karbi ragamar kasar