Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKungiyar Ma'aikatan Jinya tayi kira ga Sheikh Abdullah G/Kaya ya gaggauta janye...

Kungiyar Ma’aikatan Jinya tayi kira ga Sheikh Abdullah G/Kaya ya gaggauta janye kalamansa ya basu hakuri

Daga Muryoyi

Bayan da wani takaitaccen bayani na fitaccen Malami a Kano Sheikh Abdallah Gadon kaya ya karade kafafen sada zumunta na zamani inda ya soki ma’aikatan jinya da cewa suna aikata kazamar barna da ya hada da zinace-zinace a tsakaninsu musamman masu aikin dare

Hakan bai yiwa ma’aikatan jinyar dadi ba inda aka jiyo Shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya na jihar Kano Kwamared Ibrahim mai Karfi Muhammad ya bulla a kafafen yada labarai yana kira da babban murya ga Malam Abdullahi Gadon Ƙaya kan ya gaggauta janye kalaman da da yayi na cewa ”Ana zina da ma’aikatan jinya masu aikin dare”.

A wata hira da majiyar Muryoyi a jihar Kano Jarida Radio an jiyo Kwamared yana bayyana kalaman Malamin a matsayin mummunan zargi, cin zali da mummunar kama da aka danganta ma’aikatan jinya da shi. Ya bayyana cewa zasu dauki mataki muddin bai janye maganganun ba.

- Advertisement -

Shugaban jinyar yace ko kwanciya ma’aikatan jinya basa yi idan suna bakin aiki balle ace har sun rufe daki sun kebanta. A cewarsa ma’aikatan dare ido biyu suke zama a bakin aiki domin kula da majinyata.

Ra’ayoyin jama’a akan wannan batun

Muryoyi ta dauki kadan daga cikin martanin jama’a a Kano kan wannan batu Aminu Nasir ya rubuta cewa

“Wannan mutumin (shugaban ma’aikatan jinya) karya yake yace basa kwanciya a aikin kwana
Wallahi a asibitin kuroda munsami masu kwanciya lokacin da muka kakai Mara lfy a bangaran Yan haihuwa haka suka bar masu naquda acikin yanayi na ko sumutu ko suyi Rai ba abin da yadame su Kuma ni ganau ne ba jiyau ba wallahi” -Aminu Nasir

Usman Hassan Muhammad kuwa cewa yayi: “Bai kamata ace malamin addini ya na sakin zance yanda ya ga dama ba, wannan ba koyarwar musulunci bane.” -Usman Hassan Muhammad

Sannan sai Muhammad Mahbub da ya ce “Wallahi (Malam) yana da gaskiya….. Idan zaku gyara kawai ku gyara.” -Muhammad Mahbub

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: