An kama Wi-wi ta Miliyan 200 da aka shigo da ita Nigeria daga Ghana

Daga Muryoyi

Jami’an hukumar NSCDC a Lagos sun samu nasarar kama wasu masunta yan kasar Ghana su 9 da ake zargi sun yi yunkurin shigo da tabar Wi-wi cikin Najeriya wacce darajar kudinta ya kai Naira miliyan N200

Muryoyi ta ruwaito sunayen wadanda aka kaman sun hada da Musa, Gasie, Adotete, Sottie, Tette, Okonipa, Stephen, Toyokpti da kuma Natte dukaninsu

Da yake gabatar da wadanda aka kaman a hedkiwatar hukumar NSCDC dake Ikeja a jihar Lagos, Mista Edenabu Okoro Eweka, ya ce hukumarsu ta samu bayanan sirri akan mutanen da kuma yunkurinsu safarar tabar zuwa Nigeria ta cikin karamin jirgin ruwa.

- Advertisement -

Ya ce ba bata lokaci suka ankarar da Jami’an su dake bakin ruwa kuma sai gashi sun samu nasarar damke su.

Eweka ya kara da cewa binciken da sukayi darajar yawan tabar wiwin ya kai Naira miliyan 200

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: