Ba Fim ke bawa ƴan Fim kuɗi ba –Ahmad Nagudu ya fasa kwai tare da hujjoji

Daga Ahmad Nagudu

“Tun da na fara Fim, kawo yanzu, ban yi Fim ɗin da aka ɗauki dubu 50 ko dubu 30 ko dubu 20 aka ba ni ba, balle in yi tanadin wani abu”

Dangane da waɗannan kalaman da dattijuwar jaruma Ladin Chima ta furta da yadda mutane su ka ɗauke su, su ke kuma amfani da su wajen ɗora kafatanin ƴan Fim akan mizani guda su na zartar musu da hukunci ɗaya, na rashin kyautawa ko rashin kirki har da rashin adalci da ake kallon ƴan Fim da shi game da abun da ta yi ikirarin ana biyan ta, na fahimci akwai rashin takamaimai yadda tsarin harkar Fim a Ƙasar Hausa musamman a wajen mutanen mu na Arewa da su ke hangen abun daga nesa. Abun da mu, mu ka sani a cikin gida daban ne da wanda mutane su ke zato ko tsammani da hasashe, tun kusan kafuwar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Amma bari na takaita akan iya abun da na ke son yin martani a kan shi na biyan jarumai kuɗin Fim, wanda abun farko da ya kamata mu fara sani shine, nawa ake kashewa ne ma gaba ɗaya wajen shirya Fim ɗin sukutum ɗin sa. Domin idan aka ce kuɗin da ake kashewa wajen shirya Fim, ya kunshi tun daga samar da labari har zuwa matakin da Fim zai kammala ya shiga kasuwa ne. Kenan bayan jarumai akwai wasu da su ke zaman mahadin da sai da su ma Fim ɗin zai yiyu, wanda su ma kuma dole biyan su ake yi.

- Advertisement -

Waɗannan kuwa sun haɗa da, marubuci, darakta, mai ɗaukar hoto, mai kwalliya, mai kawo sutura, mai haska fitila, mai naɗar sauti, mai haɗa hoto, mai zanen fasta, mai kula da walwala, mai zirga-zirga, mai shiryawa, mai samar da dandali, mai kula da ci gaban shiri, makaɗi, mawaƙi, duka su na da ruwa da tsaki da rawar takawa a cikin Fim. Kuma duk biyan su ake yi.

Amma abun da ya kamata a sani anan shine, wanda ba lallai ɗan kallo ya sani ba, duka waɗannan ma’aikatan da ma ƙarin wasu da akan iya samu, da yawan adadin jaruman da za su taka rawa a cikin Fim, ƙaddara mutum 20 ko 30 ko 40, ana iya aiki da su a samar da kammalallen Fim cikakke akan kuɗin da bai wuce dubu 500 ko 600 ko 800 ko Miliyan Ɗaya ba. Fim kuma mai tsawon mintoci 150, wanda za a gutsura shi zuwa na 1 na 2 zuwa na 3 da na 4.

Idan Fim mai ɗauke da mutum 30 ko 40 da ma’aikata 20 na fili da na ɓoye, za a kashe masa kuɗi dubu 700 ko 800 zuwa miliyan 1, (wanda kuma irin waɗannan fina-finan su ne kaso ma fi yawa a masana’antar Kannywood tun samuwar ta a 1988) nawa ne kenan za a biya kowa a matsayin hakkin aikin sa?

Idan abu ba sana’a ko harkar ka ba ce, kar ka kutsa ciki ka na bayan fage ka kama hukunci ko alƙalanci a cikin ta.

Don haka a masana’antar Kannywood, ana iya shirya Fim sukutum da guda akan Naira dubu 200 kacal. Kuma ka ga manyan jarumai a ciki, kuma ya fita ya shiga kowane saƙo da loko na duniyar Bahaushe. Kuma ya na ɗauke saƙo mai girma da taɓa zuciya.

Wani zai ce to, nawa ake biyan kowa kenan kuma a kan wannan kuɗin kuma Fim ɗin ya fita da labari mai ƙarfi da jarumai manya? To, amsar ita ce ba kowa ake biya a cikin duk waɗanda aka ga bayyanar fuskokin su a cikin Fim ba. Ko kuma a cikin ma’aikatan bayan fage ba.

Me yasa hakan to? Ko kuma me ke jawo hakan? Kuma meye ribar su kenan in dai ba za a biya su ba? Akwai!

Duk wani jarumi ko jaruma da ka gani ko wani cikin ma’aikatan Fim da katon gida ko ƙatuwar mota da shiga ta alfarma, ba kuɗin Fim ba ne. Dukan su kuwa!

Ina nufin ba kuɗin da ake biyan su a Fim ne suke tarawa har ya yi yawan da za su sayi wasu abubuwan jin daɗin rayuwa ba.

Wani zai ce, “To, daga ina su ke samo kuɗin da su ke facaka da su da ake gani kenan, Ahmad?”

Babban abun da harkar Fim ke gadarwa mai yin sa shine, SHUHURA, ƊAUKAKA, SANUWA da yaɗuwar fuska ko sunan mai yin harkar, walau jarumi ko ma’aikacin bayan fage. A dalilin wannan SHUHURA da ɗaukakar, ya kan samu dimbin masoya, masu ƙaunar sa a dalilin rawar da ya ke takawa a cikin fina-finan. Masoyan nan kuma, su kan zama daga cikin dukkan rukunonin mutane a cikin duniya gaba ɗaya. Kama daga mata, maza, yara, manya manyan mutane, attajirai, masu mulki, shugabanni, sarakuna, ƴan kasuwa, ƴan siyasa da sauran su.

Wannan Soyayya ko burge su da ɗan Fim ɗin ya ke yi, sakamakon ganin shi da su ke yi a cikin wannan Fim ɗin dubu 600 ɗin nan, shi zai sa su nemi gani ko haɗuwa ko sanin sa ko kiran shi ma har gidajen su don su nuna jin daɗi da gamsuwar su kan wani abu da ya ke yi da ke ƙayatar da su. Kuma babu yadda dai, irin waɗannan mutanen za su kira ɗan Fim ko mawaƙi zuwa gare su, ya fito haka nan hannu rabbana ba tare da wani ƙunshi ko dunkulin girma ba. Wanda a dalilin hakan sai ka ga, duk wanda ya yi wa wani ɗan Fim ko mawaƙi wata gagarumar kyauta, automatically sai ka ga ya zama ubangida ko uwargijiyar wannan jarumi, jaruma ko mawaƙin. Ta yadda duk wani abu na shi idan ya tashi sai ka ga an gayyaci wannan ɗan Fim ɗin. Kuma duk wata hidima da ta tashi, ta su, sai ka ga wannan ɗan Fim ɗin cikin sabgogin su. Ba ka ankara ba, sai ka ga waɗannan mutanen sun zama kamar ƴan uwan ka, ta yadda kai ma duk wata hidima taka da ta tashi, su ma za su jiɓanci lamurran ka.

Kuma babu wani fitaccen ɗan Fim da ba shi da irin wannan (iyayen gidan) cikin rukunin mutane da na zayyana a sama. Kuma ubangida ko uwargidan ma ba ɗaya ko biyu ba. Saboda yawan masoyan su. Wani bai ma taɓa gani ko haɗuwa da wanda ya ke so ɗin ba, amma idan ya dunƙulo wata kyautar ya turo masa, sai ka ga kamar rabon gado aka yi ya turo masa na shi kason. Shi ya sa za ka ga rana tsaka mutum ya canja kamar juya bayan tafin hannu daga gaba zuwa baya.

Don haka alfarmar da ke cikin harkar Fim ta na da matuƙar yawa. Kuma hakan ma ya danganta da karɓuwa da yaɗuwar da ka yi kan wata rawa da ka ke takawa a fina-finan.

Akwai misalai da yawa da mu ka sani cikin ƴan uwan mu, ƴan Fim waɗanda aka yi wa irin waɗannan abubuwan na alfarma dalilin kasancewar su ƴan Fim. Akwai jarumin da wata mata da bai taɓa gani ba, ta aiko direba har Kano ya kawo masa kyautar mota ƴar uban su, da bakin shi ya ce wallahi bai taɓa ganin ta ba. Wannan ɗaya ne kawai.

Sannan daga yanayin rawar da ka ke takawa a cikin ayyukan ka da yawan zancen ka da ake a gari, ya kan ja hankalin wasu Kamfanoni, Gwamnatoci, Ƴan Siyasa, Ƙungiyoyi Masu Zaman Kan su na cikin gida da na waje, Hukumomi daban-daban, su kan nemi jaruma, jarumi ko mawaƙi ta hanyar Furodusa ko Darakta don su yi amfani da suna ko fuskar sa wajen yaɗa manufofin su. Ga nan misalai nan da yawa a cikin ƴan Fim da mawaƙan nan na mu.

To, wannan ya sa kowa ke dagewa wajen yin ayyuka da motsi don a ji shi a gan shi, don ya samu wannan recognition ɗin daga wajen wasu da za su iya ba shi aikin da ba na Fim ba.

Kuma ban ware ba, babu wani jarumi da ke Kannywood a yanzu da sunan shi ke amo wanda in ya samu wata dama, ba ya assasa wani abun da zai dinga kawo masa kuɗin shiga a wajen Kannywood ɗin ba. Kenan ita harkar sila ce kawai, amma ba ita ke kawo maka kuɗin ba. Misali ni a yanzu, ta dalilin Social Media na haɗu da mutanen da su ka ba ni ayyukan da na samu alherin da tsakani na da harkar sai dai son barka. Domin har na haɗu da ubangida cikin manyan mutane a nan Arewacin Najeriya, kuma ya zama komai nawa.

Ni na san jarumai da yawa waɗanda don kar sunan su ya yi kasa a mance su, damarmaki su dinga tsallake su ya sa su ke Fim, ba don abun da za a ba su ba.

An sha kiran Ali Nuhu, Adam A. Zango, Sani Danja, Yakubu Muhammad, Sadiq Sani, Zahraddeen Sani, Baballe Hayatu, Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Ibro, Daushe, Nuhu Abdullahi, Fati Washa, su zo su yi aiki, su taka rawa a Fim, amma su tafi ba tare da an ba su ko sisin kwabo ba. Saboda kawai mai Fim ɗin wataƙila zai yi don neman kasuwa ne ko kuma saboda kusancin da ke tsakani. Musamman Ali Nuhu da Sani Danja da Zango, sun fi kowa yi wa Daraktoci da Furodusoshi wannan abun. Don ban san sau nawa Ali ke karɓar aikin Fim, ba tare da an yi ciniki da shi ba, sai an gama sai ya ce da mai Fim ɗin Allah ya kawo kasuwa. Ya bar kuɗin, ya yi masa a matsayin gudummowar sa.

Akwai manyan jaruman nan da dama, irin su Hajarah Usman, Saratu Daso, Marigayiya Mai Aya, Asma’u Sani da Ladidi Fagge da su Bashir Nayaya, idan ba ka da ko sisi ma, ka same su ka yi musu bayani, wallahi tsaf, za su yi maka aiki kuma ba tare da sun damu ba. Meye a ciki?

Don haka kamar yadda na faɗa a sama, ba Fim ke bawa ƴan Fim kuɗi ba. Harkokin da su ke yi waje dalilin sanuwar fuskar su, akan doron wannan alfarmar su ke rayuwa. Kuma nima na ci wannan gajiyar ba kaɗan ba, har yanzu kuma ina kan cin ta.

Game da jarumai mata kuwa, duk da ba zan bada shaida akan abun da ban sani ko gani ba, amma a ƙaramin misali, ko budurwa ce a unguwar ku (kai mai karatu) kai ko ma a gidan ku ne, aka ce Samari na zuwa zance wajen ta, akwai yiyuwar wani a ƙoƙarin neman Soyayyar ta, zai iya saya mata waya, sutura, kayan kwalliya, yi mata Anko, ba ta kuɗi da sauran su. Kuma ko da akwai wata alaƙa ko wata manufa ce da shi, amma dai ya na yi mata. To, ƴar unguwar ku ma kenan, da iya yankin ku, a garin ku kawai aka santa. Ina ga Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Fati Washa, Maryan Babban Yaro, Zeepretty, Ummi Rahab, Bilkisu Shema, Bilkisu Abdullahi,Nafisa Abdullahi da sauran su? Wani haka kawai saboda ya na son wata jarumar Fim ko tana burge shi, ba ma a Najeriya ya ke ba, zai kira ka ya nemi ka isar mata da wani saƙo. Idan ya jefe ta da wata kyautar, sai ka rasa ta in da ma zaka fara bayar da labarin. Ka rabu kuma da NAMIJI akan abun da ya ke so da ƙauna. Babu abun da ba zai iya yi a kai ba. Mu maza mun san wannan, musamman idan ka na da wadata.

Akwai da dama wallahi cikin ƴan matan Fim ɗin nan, da masoyan su ke musu kyautar motoci ko wasu abubuwa ko kuɗaɗe ba tare da sun taɓa ganin su ba, kuma daga mata da maza.

Ni nan, na shirya fina-finai da dama sun kai 6, wanda babu wanda na taɓa kashe kuɗin da ya kai dubu 500 a kan su. Na ƙarshen nan, shine A DALILIN WASA. Wanda jarumai manya ne a cikin sa, amma gaba ɗaya ban kashe dubu 200 ba.

Girman ka a fagen harkar sana’a ko aiki da sanuwar ka, shine ke auna mizanin alheri da damarmakin ka. Kuma kuɗin da ka ke samu, ka na da ƴan uwa da iyalai da dangi, kai ma za ka ji da su ne, ko kuma za ka yi ta kashewa wasu don ku na harka ɗaya da su?

Akwai abun da sadaukarwa da sha’awa da ra’ayi ne a cikin sa, ba wai zallar kuɗin da za a biya ka ba. Akwai da yawa a cikin ƴan Fim da na sani waɗanda ta sanadin harkar Fim su ka samu damarmakin da su ka bunkasa da gawurta, su ka samu alheri, wanda kuma harkar ta daina yi da su saboda zamanin su ya wuce. Amma sai su ka yi amfani da wadatar su wajen dawowa fagen don dai a ci gaba da jin amon su. Akwai waɗanda ma a cikin su, da in sun ji za a yi wani babban Fim da zai yi motsi sosai, su su ke biyan masu Fim ɗin ma don a ba su gurbi a ciki. Ko kuma idan su ka ga Furodusa mai ƙaramin ƙarfi ne kuma ya taso da nasibi, sai su saka hannu a kan shi, su yi amfani da kuɗin aljihun su da su ke samu daga wasu harkokin, su tallafa masa ya mike don ya ci gaba da yi da su. Mata da maza su na yin hakan kuma. Kai hatta wasu a cikin mawaƙan mu ma, su na yin haka. Musamman a cikin irin shirye-shiryen nan masu dogon zango na manyan gidajen Talabijin ɗin nan.

Don haka a masana’antar Kannywood, gudun yada ƙanin wani ake yi. Kowa ƙoƙari ya ke yi, ya yi abun da zai samu ya tsira don ya rayu cikin rufin asiri. Kowa kan sa ya ke nemawa. Fafutukar da ake yi kullum kenan shine ta yaya za a samu kusanci da shiga cikin sabgogin da za a samu a rabauta da wani abu. Wannan ya sa kusan duk wani mai sananniyar fuska, ya na da wani ɗan Siyasa da ya ke jingine da shi a matsayin mai gida ko wanda ya ke tallata manufofin sa. Wanda kuma wannan ya sa yanzu da dama cikin ƴan Fim da mawaƙa su ke samun damarmakin naɗa su akan wasu mukamai daga matakin Jiha har Tarayya. Ashe in da ba ka dage akan aikin ka, an ji ka, an san ka ba, da babu wanda zai damu da kai balle har a dinga damawa da kai ba.

Daga ƙarshe, ko ba a biya Ladin Cima kuɗin aikin fitowa a Fim ba, akwai kuma kuɗaɗe ta dalilin Fim ne ta same su, wanda ƴan Fim ɗin ne su ka ba ta, ko kuma su ka yi mata sanadin samun su. Ciki kuwa har da Hadiza Gabon da ta bata kyautar 250K a wajen ɗaukar shirin Gidan Badamasi. Da kuma gidan da mawaƙi Kamilu Koko ya bata akan ta zauna har ƙarshen rayuwar ta, kamin daga bisani, ta dai dalilin Fim ɗin ta samu na ta muhallin na kan ta, ta fita daga na shi. Rarara ya taɓa bata kyautar kuɗi dubu 100.

Suna na Ahmad Nagudu

Mawaƙi
Furodusa
Marubuci
Ɗan Jarida
Ƙwararre A Kan Harkokin Yanar Gizo

10-02-2022

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: