Budurwa zata bawa Saurayin ta kyautar Naira miliyan 5 tsabar soyayya
TO FA: Wata budurwa ta ce da zata samu Miliyan 5 da Dubu 100 kawai zata dauka ta baiwa Saurayin ta ragowar canjin miliyan 4.9 din ya yi sha’aninsa dasu saboda yadda take masifar son shi…
Haka dai wata Budurwa mai suna Ummu Abieha ta rubuta a shafinta na Facebook a cikin harshen turanci….
Da zan samu miliyan Biyar (5M) a yanzu aikuwa da dubu Dari kawai zan dauka a ciki in baiwa Saurayi na duka ragowar kudin (wato 4.9M) yaje yayi bukatunsa dasu, saboda yadda nake masifar son shi.
Dubu 100 ma zan saka Data ne kawai don in riga ganin Status dinsa.
- Advertisement -
Ba zaku gane bane Ina masifar son gayen nan…