Budurwar da zata iya bawa Saurayin ta kyautar 5M ta fadi yadda zata samu kudin

Daga Muryoyi

Anyi ca kan budurwar da tayi raha cewa da zata samu Miliyan 5 da Dubu 100 kawai zata dauka ta baiwa Saurayin ta ragowar canjin miliyan 4.9 din ya yi sha’aninsa dasu saboda yadda take masifar son shi…

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayinsu har ta kai ga wasu na ganin ina ma dai yan matan Arewa zasu dauki irin kyawun nufin taimakawa miji da wannan yarinya ta nuna.

Sanin kowa ne a matan mu na yanzu musamman Hausawa jira suke ka basu ‘nasu nasu ne amma naka nasu ne’ ko biliyan wata zata samu ba zata tuna da miji ba saboda haka lallai wannan yarinya ta nuna tana da faffadan zuciyar taimakawa mijinta a gudu tare a tsira tare Allah yasa yayi mata halacci. Ra’ayin wasu daga ciki

- Advertisement -

Wasu kuma na ganin ba zata iya ba fade kawai take ayi raha saboda matan yanzu masu jira ayi masu komi ne “macen da zata iya wannan sai yan zamanin iyaye da kakanni amma ba na yanzu ba…” inji wasu

To sai dai ganin cewa budurwar ta basu sha’awa yadda ta yi wannan tunani har suka rika tambayar ina zata samo kudin?

To aikuwa dai wannan budurwa dama ance Juma’a mai kyau daga Laraba ake gane ta Ummu Abieha dai yar kasuwa ce dake sana’ar saida Awarar yan gayu don haka ku garzaya ku sayi awara domin ta tara kudi ayi yar kure muga ko zata kashewa saurayin kudi a wajen lefe 😆

Ana iya tuntubar ta domin odar Awara a +234 817 484 4192

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: