Daga Muryoyi
Kimanin hukumomin gwamnati da kamfanoni 42 mallakin gwamnatin tarayya za a cefanar a wannan shekarar in ji hukumar kula da kamfanonin gwamnati.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacinda da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke kawowa karshe ba tare da ya tada mafi yawa daga cikin kamfanoni kasar da yayi alkawarin zai tada ba a lokacin yakin neman zabe
Kamfanonin da za a cefanar sun hada da kamfanin makamashi 11, da kuma 10 daga bangaren masana’antu da aikace-aikace, sai guda takwas daga bangaren noma da aikace-aikacen cikin gida,
- Advertisement -
Kazalika za a sayar da kamfanoni 13 a bangaren ayyukan more rayuwa da kawace tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu
Majiyar Muryoyi ta ruwaito sanarwar tace mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci sayarwar